Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Matatar Man Fetur ta Dangote na duba yiwuwar taƙaita sayar da man fetur ga manyan ’yan kasuwar mai da ke ci gaba da shigo da man fetur daga ƙasashen waje zuwa Nijeriya.
Matakin da ake tunanin zai fara aiki tun cikin wannan makon, idan ba a samu wani sauyi a ƙarshen shawarwarin da ake yi ba, ya samo asali ne daga damuwar da matatar ke da ita kan ingancin man fetur, gaskiyar yadda ake gudanar da kasuwa da kuma kare mutuncin kayayyakin da ake sayarwa da sunan Dangote.
Majiyoyin da suka san matsayar matatar sun ce babbar damuwar ita ce yadda wasu ’yan kasuwa ke haɗa wasu man fetur da aka shigo da su daga waje, waɗanda ake zargin ba su da inganci, da man fetur da suka saya daga Matatar Dangote, kafin su rarraba shi ga masu amfani.
Matatar na fargabar cewa irin wannan aiki na iya sa ya yi wahala a bambance tsakanin man fetur da ta samar kai tsaye da kuma wanda wasu ’yan kasuwa suka sake sarrafawa ko haɗawa da wasu kayayyaki.
Wata majiya da ke da masaniya kan matsayar matatar ta ce, “Yana da wuya a fahimci dalilin da zai sa mu kashe makudan kuɗi wajen samar da ingantaccen man fetur ga ’yan Nijeriya, sannan a haɗa shi da man da aka shigo da shi wanda ba a tabbatar da ingancinsa ba, daga bisani a danganta sakamakon da sunan matatar.”
Matatar ta kuma nuna damuwa kan rashin samun cikakken ɗakin gwaje-gwaje na zamani da kuma isasshen tsarin tabbatar da ingancin man fetur da ake shigo da shi daga ƙasashen waje a wajen hukumar da ke kula da harkar man fetur. A cewarta, hakan na iya rage ƙarfin hukumar wajen gudanar da gwaje-gwaje masu zaman kansu domin tabbatar da cewa man fetur da ake shigarwa Nijeriya ya cika ƙa’idojin inganci da aka gindaya.
Wannan batu ya taso ne a daidai lokacin da ɓangaren rarrabawa da sayar da man fetur a Nijeriya ke fuskantar gagarumin sauyi, daga dogaro da shigo da mafi yawan man fetur daga ƙasashen waje zuwa ƙara amfani da ƙarfin matatun mai na cikin gida.
Matatar Man Fetur ta Dangote, wadda ke da ƙarfin tace gangar ɗanyen mai 700,000 a kowace rana, ta zama ɗaya daga cikin manyan masu samar da man fetur da sauran kayayyakin da ake tacewa a Nijeriya da kuma kasuwannin duniya. Kamfanin na cewa kayayyakin da yake samarwa sun cika ƙa’idojin inganci da ake amfani da su a kasuwannin duniya.
A baya-bayan nan, Hukumar Kula da Makamashin Amurka (EIA) ta bayyana Matatar Dangote a matsayin ɗaya daga cikin manyan abubuwan da suka taimaka wajen ƙaruwa sosai a yawan kayayyakin man fetur da Nijeriya ke fitarwa ta teku.
Bayanan hukumar sun nuna cewa yawan kayayyakin man fetur da Nijeriya ta fitar ta teku ya kai matsakaicin ganguna 561,000 a kowace rana a zangon biyu na shekarar 2026, idan aka kwatanta da matsakaicin ganguna 79,000 a kowace rana a shekarar 2023.
Rahoton ya kuma ce man jiragen sama da Matatar Dangote ke samarwa ya ƙara samun karɓuwa a kasuwannin duniya, ciki har da Amurka da Turai. Matatar ta kuma ƙara ƙarfafa matsayinta a matsayin babbar matatar da ke fitar da man jiragen sama zuwa Turai daga wajen nahiyar, inda ta kasance kan gaba na tsawon watanni a jere, har ta zarce wasu daga cikin ƙasashen da aka daɗe suna fitar da man jiragen sama daga Amurka da Gabas ta Tsakiya.
