Daga MUHAMMAD SADISU ABUBAKAR Birnin Kebbi
Matar Gwamnan Jihar Kebbi, Hajiya Nafisa Nasir Idris, ta bai wa mata shawarar zuwa asibiti a ko wani wata domin binciken ko suna da alamun kamuwa da cutar sankara, (cancer), domin a magance ta nan ta ke.
Hajiya Nafisa ta jagoranci tattaki na kilomita biyu daga Gidan Gwamnati zuwa filin wasa na Haliru Abdu da ke Birnin Kebbi ranar wannan Talata, da nufin ankarar da jama’a illolin cutar sankara.
A lokacin tattakin wanda ƙungiyar ta wadda ba ta gwamnati ba, mai suna, NANAS Foundation, ta shirya, Hajiya Nafisa ta bayyana cewar ana magance sankara muddin aka gano cutar a jikin ɗan-Adam da wuri.
Ta yi tambihi ga mata da su rika zuwa asibiti ana binciken su, ta na mai cewar, kamuwa da cutar sankara, ba zuwan ajalin mutuwa ba ke nan, saboda haka wajibine mata su dinga zuwa asibiti ana dubasu ko wani wata, aga halin da su ke ciki.
Hajiya Nafisa ta ce, an keɓe watan Oktoba na kowace shekara domin a yi tattaki da nufin ankarar da jama’a su kiyaye da kamuwa da cutar sankara, sannan kuma a taimaka ma waɗanda suka kamu da ita.
Ta yaba ma mijinta Gwamna Nasir Idris dangane da taimakon da yake bayarwa wurin kula da lafiyar al’ummar jihar Kebbi.
Matar Gwamnan ta ce maigidanta ya ɗora muhimmanci ƙwarai da gaske a kan kawar da cutar sankara ta hanyar bada cikakken goyon baya da taimakon da ake buƙata wurin hana kamuwa da cutar da kuma yaɗuwar ta da kuma yi ma masu ita magani da kuma taimaka ma su, wurin wanzar da jin-dadin rayuwarsu ta yau da kullum.
A lokacin tattakin, Hajiya Nafisa a ƙarƙashin NANAS Foundation, ta bada gudunmawar kudi Naira miliyan Ashiri (N20 miliyan) ga mata masu sana’oi domin bunƙasa kasuwanci su.
Shi kuma a nasa jawabin, Kwamishinan kiwon lafiya na Kebbi, Sama’ila Yakubu Augie, ya miƙa godiya ne zuwa ga matar gwamnan a kan shirya tattakin da ta yi shekara uku a-jere tana yi da nufin ilmantar da jama’a illar cutar sankara, da kuma hanyoyin da za a bi wurin kawo ƙarshenta.
Kwamishinan ya jinjina ma Gwamna Nasir Idris akan inganta harkokin kiwon lafiya zuwa matsayin abin yabo.
