
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rundunar ‘Yan sanda a Jihar Zamfara, ta ce ta kama wani matashi bisa zargin sa da hannu a wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta da ke nuna yana rera waƙar kira da a kashe Kiristoci.
Rahotanni sun ce, bidiyon ya nuna matashin sanye da kayan agajin Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa’iƙamatus Sunnah (JIBWIS), reshen Jihar Zamfara, tare da wasu kakwarorinsa da wasu ɗaliban makarantun Islamiya biyu a Ƙaramar Hukumar Maradun da ke jihar. An ruwaito cewa, sai da JIBWIS ta kama matashin mai suna Unar Ibrahim Gandi Maradun kafin daga bisani ta damƙa shi ga ‘yan sanda domin a gudanar da bincike akansa.
Da yake ganawa da manema labarai a Gusau a ranar Talata, Kwamishinan ‘yan sandan, Muhammad Bello, ya ce rundunar tana aiki tuƙuru wajen bai wa mazauna kariya ba tare da la’akari da bambance-bambancen addini ba. A cewarsa, bidiyon ya ƙunshi kalamai kamar, “A ba mu bindiga, mu je mu kashe Kiristoci.” Rundunar ta ce ta tura jami’anta ne leƙen asiri domin gano yadda al’amarin auku a dokance yayin bincike.
Bincike ya nuna cewa an ɗauki bidiyon ne a ranar Juma’a, 23 ga Oktoba, 2026, a lokacin da mai laifin ke kan hanyar zuwa masallacin Aliyu Ibn Abi Thalib. An ce shi da waɗanda suke tare da shi ne suka bayar da tsaro yayin sallar Juma’a da wa’azi da aka gudanar a yankin. Makarantu biyu da aka alaƙanta da bidiyon sune Nurul Islam Islamiya da Aƙidatul Sahiha Islamiya, waɗanda suke Ƙaramar Hukumar Maradun, wato kimanin nisan kilomita 120 daga Gusau.
A yayin bincike, rundunar ta tattauna da jagororin JIBWIS a matakan jiha da ƙasa. A cewarta, ƙungiyar ta nesanta kanta daga abin da wanda ake zargin ya yi a bidiyon da kuma ɗaukar da aka yi. Sannan, binciken ‘yan sanda ya nuna cewa an haifi matashin ne a ranar 15 ga Satumba, 2004 kuma ya halarci makarantun Muelledi Model Primary School da Government Day Secondary School dukkansu a Maradun.
Kazalika, ‘yan sanda sun ce ya fara aikin agaji da JIBWIS ne a shekarar 2025 kuma a kwanan nan ya samu gurbin karatu a Jami’ar Jihar Zamfara da ke Talata Mafara domin yin digiri a Tsangayar Koyon Aikin Jarida. Kwamishinan ya bayyana cewa ana cigaba da gudanar da bincike akansa inda da zarar an kammala, za a maka shi a kotu domin ya fuskanci hukuncin da dokar ƙasa ta tanada, yana mai tir da halin wanda a cewarsa zai taimaka wajen hura wutar gaba tsakanin mabiya addinai da zama barazana ga zaman lafiyar al’umma.
Har ila yau, ya kirayi jagororin addini, iyaye, jagororin makarantu da masu ruwa da tsaki acikin al’umma da su riƙa yaɗa muhimman ababen da za su taimaka wajen girmama juna da ɗabi’u na gari musamman acikin matasa, sannan su ƙaurace wa yaɗa dukkan wani rahoto ko labari na ƙarya da zai yamutsa halin amincin zamantakewa ko hargitsa al’amura.
