An kori jami’an EFCC sama da 40 kan cin hanci — Olukoyede

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Yaƙi da Masu Karya Tattalin Arziki ta ƙasa (EFCC) ta ce ta kori fiye da ma’aikatanta 40 cikin shekaru biyu da rabi da suka gabata, sakamakon zargin cin hanci da sauran laifukan da suka shafi kuɗi.

Shugaban hukumar, Ola Olukoyede, ne ya bayyana haka a Abuja yayin ganawarsa da shugabannin kafafen yaɗa labarai da ’yan jarida.

Ya ce fiye da biyar daga cikin waɗanda aka kora na fuskantar shari’a, yayin da ake shirya takardun wasu domin gurfanar da su gaban kotu.

Olukoyede ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin tabbatar da cewa jami’an EFCC suna bin ƙa’idojin rike gaskiya da amana, musamman ganin cewa hukumar ce ke yaƙi da cin hanci a ƙasar.

Ya kuma ce hukumar ta ƙara tsaurara matakan da ke tabbatar da ɗa’a da gaskiya a tsakanin ma’aikatanta, ciki har da sabuwar dokar karɓar kyaututtuka da bayyana dukiyoyi.

A cewarsa, ba zai yiwu jami’in EFCC ya yi yaƙi da cin hanci ba, alhali shi kansa yana aikata irin wannan laifi.

A wani ɓangare na jawabin, Olukoyede ya bayyana cewa EFCC ta ƙwato Naira tiriliyan 1.23, da Dala miliyan 684.48, da Fam 373,905 da Yuro miliyan 9.34 tsakanin 1 ga Oktoba 2023 zuwa 30 ga Yuni 2026.

Ya ce daga cikin kuɗin Naira da aka kwato, Naira biliyan 397.26 an ƙwato su ne kai tsaye ga Gwamnatin Tarayya, yayin da Naira biliyan 836.34 aka kwato a madadin ma’aikatu da hukumomin gwamnati da sauran waɗanda suka dace.

Shugaban EFCC ya kuma bayyana cewa an rarraba Naira biliyan 661.32 da kuma Dala miliyan 492.37 daga cikin kuɗaɗen da aka ƙwato ga waɗanda suke da haƙƙin karɓar su a cikin lokacin.

By ukarofi

Leave a Reply