Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin samar wa ƙwararrun ’yan Nijeriya damar aiki a ƙasashen waje

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da wani sabon shiri mai suna “Hire from Nigeria”, domin bai wa ƙwararrun ’yan Nijeriya damar yi wa kamfanoni da masu ɗaukar ma’aikata na ƙasashen waje aiki daga cikin ƙasar.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan ranar Litinin yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a ofishinsa da ke Abuja.

Idris ya ce ƙaddamar da shirin wani muhimmin mataki ne na sanya ɗaya daga cikin manyan kadarorin Nijeriya, wato ɗimbin al’ummarta masu ƙwarewa, a sahun gaba wajen hulɗar tattalin arzikin ƙasar da duniya.

Ya ce yawan matasan Nijeriya, da ɗimbin ƙwararrun ma’aikata, tare da bunƙasar fasahar zamani, sun bai wa ƙasar damar yin gogayya da sauran ƙasashe a fagen tattalin arzikin duniya.

A cewarsa, makomar tattalin arzikin Nijeriya za ta ƙara dogara ne kan ƙwarewa, ƙirƙire-ƙirƙire, fasaha da kuma ƙwazon jama’a.

“Makomar tattalin arzikin Nijeriya za ta ƙara dogara ne kan ƙwarewa, ƙirƙire-ƙirƙire, fasaha da kuma ƙwazon jama’armu. A shirye Nijeriya take ta yi gogayya a fagen duniya, kuma ƙwararrun ’yan Nijeriya suna shirye su yi aiki. Ya kamata duniya ta mayar da hankali kan Nijeriya,” inji shi.

Ministan ya ƙara da cewa shirin ya haɗa Ma’aikatun Tarayya na Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, da Ilimi, da Hukumar National Talent Export Programme (NATEP), da shirin iDICE, tare da kamfanoni masu zaman kansu.

Ya ce manufar haɗin gwiwar ita ce samar da wata hanya da za ta haɗa ƙwararrun ’yan Nijeriya da kamfanoni da masu neman ƙwararrun ma’aikata a faɗin duniya.

Idris ya ce shirin ya yi daidai da Ajandar Sabunta Fata ta Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, da kuma burin Gwamnatin Tarayya na samar da guraben aikin yi miliyan ɗaya ta hanyar fitar da ayyukan ƙwararru zuwa kasuwannin ƙasashen waje.

“Ba sai matashi ɗan Nijeriya ya bar ƙasar ba kafin ya samu damar shiga harkokin tattalin arzikin duniya. Idan aka ba shi ƙwarewar da ta dace, ababen more rayuwa, ƙa’idojin sana’a da damar shiga kasuwanni, ’yan Nijeriya za su iya rayuwa, su yi aiki kuma su samu kuɗi a nan gida, yayin da suke yi wa abokan ciniki da masu ɗaukar ma’aikata a faɗin duniya aiki,” inji shi.

Shi ma Ministan Ilimi, Dakta Maruf Tunji Alausa, ya ce Ma’aikatar Ilimi tana ɗaukar matakan inganta ƙwarewar ’yan Nijeriya ta hanyar bunƙasa tsarin koyarwa, koyar da sana’o’i da dabarun fasahar zamani, tare da horar da jama’a bisa buƙatun masana’antu.

Ya ce manufar ma’aikatar ita ce tabbatar da cewa duk inda ake neman ƙwararrun ma’aikata a duniya, ’yan Nijeriya sun samu horon da ya dace, takardun shaidar ƙwarewa kuma suna shirye domin samun aikin.

“Manufar Ma’aikatar Ilimi ita ce, a duk inda ake neman ma’aikata a duniya, muna son ’yan Nijeriya su samu horo, su samu takardar shaidar ƙwarewa kuma su kasance a shirye don a ɗauke su aiki,” inji shi.

A nata ɓangaren, Ministar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Dakta Jumoke Oduwole, ta ce gangamin zai taimaka wajen samar da ayyukan yi ga matasan Nijeriya, da ƙara fitar da ayyuka zuwa ƙasashen waje, tare da jawo zuba jari.

Ta ce shirin “Hire from Nigeria” ya wuce kamfen na wayar da kai kawai, domin wani tsari ne na ƙasa da aka tsara domin bunƙasa tattalin arzikin Nijeriya.

“Shirin ‘Hire from Nigeria’ ya wuce kamfen na wayar da kai kawai; shiri ne na ƙasa da aka tsara domin bunƙasa tattalin arziki,” inji ta.

Oduwole ta ƙara da cewa ana sa ran gabatar da kamfen ɗin a taron Majalisar ɗinkin Duniya karo na 81, inda Nijeriya za ta bayyana wa masu ɗaukar ma’aikata na duniya fa’idar ɗaukar ƙwararrun ’yan Nijeriya aiki.

Tun da farko, Babbar Mataimakiya ta Musamman kan Sadarwa ta Dabaru da NATEP, Misis Olajumoke Dan-Okayi, ta ce shirin zai taimaka wajen magance matsalolin da ke hana ƙwararrun ’yan Nijeriya samun damar shiga kasuwar ayyukan yi ta duniya.

Ta ce babban ƙalubalen ba rashin ƙwarewa ko buri ba ne, sai dai matsalar yadda za a gano ƙwararrun ’yan Nijeriya, a amince da su, sannan a ba su damar shiga kasuwannin duniya.

“Ba ƙwarewa ce matsalar ba, kuma ba buri ba ne. Matsalar ita ce yadda za a gano ƙwararrun ’yan Nijeriya, amincewa da su da kuma samun damar shiga kasuwannin duniya. Don haka, shirin ‘Hire from Nigeria’ yana da ayyuka uku masu sauƙi: ya sauƙaƙa wa duniya gano Nijeriya, ya sauƙaƙa amincewa da ƙwararrun ’yan Nijeriya, sannan ya sauƙaƙa ɗaukar ’yan Nijeriya aiki,” inji ta.

Ana sa ran shirin zai samar da wata gada tsakanin ƙwararrun ’yan Nijeriya da masu ɗaukar ma’aikata, kamfanoni masu neman ma’aikata, masu zuba jari da kuma kasuwannin ƙasashen waje, domin bai wa ’yan ƙasar damar cin gajiyar tattalin arzikin duniya ba tare da dole sai sun bar Nijeriya ba.

By ukarofi

Leave a Reply