Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda 1,487, sun ceto mutane 777 cikin watanni biyu

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shalkwatar Tsaron Nijeriya (DHƙ) ta ce rundunar sojin ƙasar ta gudanar da ayyukan tsaro 7,062 a faɗin ƙasar cikin watannin Yuli da Agusta, inda ta hallaka ’yan ta’adda da ’yan tawaye 1,487 tare da ceto mutane 777 da aka yi garkuwa da su.

Daraktan Yaɗa Labarai na Shalkwatar Tsaron Nijeriya, Manjo Janar Samaila Uba, ne ya bayyana hakan ranar Talata a Abuja yayin taron haɗin gwiwa na hukumomin tsaro.

Ya ce ayyukan sojin sun haɗa da na ƙasa, sama da ruwa, inda aka mayar da hankali kan yaƙi da ta’addanci, ’yan bindiga, garkuwa da mutane, safarar makamai, satar ɗanyen mai da sauran laifuffuka.

A cewarsa, a yayin samamen da aka gudanar a sassa daban-daban na ƙasar, an kama mutane 354 da ake zargi da hannu a ayyukan ta’addanci da sauran laifuka, yayin da aka ƙwato bindigogi 91, harsasai 1,331 da kuma abubuwan fashewa 44.

Manjo Janar Uba ya ce manufar ayyukan ita ce raunana ƙarfin ƙungiyoyin masu aikata laifuka, katse hanyoyin da suke samun kayan aiki, ceto waɗanda aka yi garkuwa da su, da kuma kare rayuka da muhimman ababen more rayuwa.

Ya ce rundunar sojin Nijeriya na ci gaba da ƙoƙarin fatattakar duk wani nau’in laifi da ke barazana ga tsaron ƙasar.

A cewarsa, an ci gaba da kai hare-hare a dukkan shiyyoyin ƙasar, musamman kan ƙungiyoyin ’yan ta’adda, ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane, masu fashi da makami da sauran masu aikata laifuka.

Haka kuma, ya ce dakarun tsaro sun ɗauki matakan daƙile tashe-tashen hankulan ’yan aware, satar ɗanyen mai da kuma ayyukan tace man fetur ba bisa ƙa’ida ba.

A yankin Arewa maso Gabas, Manjo Janar Uba ya ce sojojin Operation HADIN KAI sun hallaka mayaƙan Boko Haram da ISWAP 309, tare da kama wasu da ake zargi da taimaka musu da kuma samar musu da kayan aiki.

Ya ƙara da cewa ƙarin matsin lamba da dakarun suka yi wa ƙungiyoyin ’yan ta’adda ya tilasta wasu daga cikin mayaƙan da iyalansu miƙa wuya a wurare daban-daban.

Haka kuma, an ceto ɗaruruwan mutane daga maɓoyar ’yan ta’adda, yayin da dakarun tsaro suka gudanar da samame bisa bayanan sirri, kwantan-ɓauna da ayyukan ceto a wasu yankuna.

A cewarsa, waɗannan ayyuka sun taimaka wajen tarwatsa hanyoyin zirga-zirga da hanyoyin samar da kayan aiki ga ’yan ta’adda da sauran ƙungiyoyin masu aikata laifuka.

Rundunar Sojin Sama kuma na ci gaba da bai wa dakarun sojin ƙasa tallafin kai hare-hare da tattara bayanan sirri ta sama, wanda hakan ya ƙara musu damar gano wuraren da masu tayar da zaune tsaye ke buya.

A ɓangaren samar da zaman lafiya, Manjo Janar Uba ya ce an gudanar da shirye-shiryen tattaunawa guda tara tare da tarukan tattaunawa guda 15 da shugabannin gargajiya da na addini.

Ya ce rundunar ta kuma fitar da sanarwar manema labarai guda 137, yayin da aka gano tare da daƙile bayanan ƙarya guda 13.

Shalkwatar Tsaron Nijeriya ta ce ba a samu wata babbar barazana ta tsaro a kan iyakokin ƙasar ba a cikin lokacin da ake magana a kai.

Haka kuma, ta ce ba a samu lalata muhimman ababen more rayuwa, tserewar fursunoni daga gidajen yari, lalata manyan bututun mai, layukan dogo ko manyan tituna ba.

Manjo Janar Uba ya danganta nasarorin da rundunar ta samu da haɗin gwiwar rundunonin soji, sauran hukumomin tsaro da kuma goyon bayan al’umma.

Ya buƙaci ’yan Nijeriya su ci gaba da kasancewa cikin taka-tsantsan tare da bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanan sirri cikin lokaci domin taimakawa wajen yaƙi da rashin tsaro.

Ya kuma yaba wa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Babban Kwamandan Rundunar Sojin Nijeriya, kan goyon baya da jagorancin da yake bayarwa wajen ƙarfafa rundunar da inganta ayyukan tsaro.

Haka kuma, ya yaba wa jami’an soji da sauran hukumomin tsaro bisa sadaukarwar da suke yi, tare da kira ga kafafen yaɗa labarai da su ci gaba da bayar da sahihan rahotanni kan ayyukan tsaro tare da nuna ƙwarewa da sanin ya kamata.

By ukarofi

Leave a Reply