Abin da ya sa Tinubu ba ya son a fitar da rahotonsa na Amurka – Fadar Shugaban Ƙasa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Fadar Shugaban Ƙasa ta yi bayanin abin da ya sa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba ya goyon bayan fitar da cikakken kundin rahoton da hukumomin kiyaye dokokin Amurka suka riƙe, tana mai cewa akwai keɓancewa a ƙarƙashin dokokin ‘yancin samun bayanai (FOIA) na Amurka kuma ba su kai ga ɗora aikata babban laifi ba akan shugaban Nijeriyar.

Fadar, a wata sanarwa da ta fitar yayin sabunta muhawara acikin al’umma kan batun, ta ce ana gudanar da shari’ar ne a wata kotun Gunduma da ke ƙasar Kolombiya a matsayin rikicin zamantakewa kan samun duba kundaddakin gwamnati. Ta bayyana cewa, babu ɗaya daga cikin kotun ko wata hukumar gwamnatin Amurka da ta gano Tinubu yana da hannu a wani babban laifi a lamarin.

Fadar ta ce rikicin ya samu asali ne tun a shekarar 2022, a lokacin da Aaron Greenspan ya miƙa buƙatar FOIA ga hukumomin gwamnati da ke neman samun kundaddakin bayanai na gwamnatin ƙasar da suka shafi Tinubu.

A cewar sanarwar, bayan wasu hukumomi sun riƙe bayanai ko ƙin tabbatarwa ko musanta ire-iren waɗannan rahotanni akwai su ko akasin haka, Greenspan ya fara ɗaukar matakin shari’a a kotun Kolombiya a 2023. Daga bisani kotun ta ƙyale Tinubu ya shiga cikin shari’ar a matsayin mai shiga tsakani.

Haka kuma, fadar ta tunatar da abin da ya faru a shekaru 23 da suka gabata a ranar 4 ga Fabarairun 2003, inda Ofishin Jakadancin Amurka a Legas ya aike da wata takarda ga tsohon Sufeto-Janar na wancan lokaci, marigayi Tafa Balogun, wadda a ciki ya ce wasu bayanai na FBI sun gano cewa babu wani rahoton kamen aikata mugun laifi ko izinin neman kama Tinubu, wanda a lokacin shi ne gwamnan Jihar Legas.

A yanzu, fadar ta bayyana cewa hukumomin gwamnatin Amurka sun kafu akan matakin shari’a da ke barin hukumomi a wasu halaye na kada su tabbatar ko musanta wanzuwar kundaddakin bincike domin hakan dama ce ta bayar da kariya ga jami’an kula da biyayya ga doka, majiyoyin sirri da dabarun bincike.

Sannan, fadar ta ce FBI da DEA bisa biyayya ga umarnin kotu, sun fitar da shafi 399 na kundaddakin duk da cewa an cire wasu wurare a ƙarƙashin dokar keɓancewa ta Amurka. Saidai Greenspan ya ƙalubalanci matakin hukumomin na cire wasu guraren.

A cewar fadar shugaban ƙasar, FBI da DEA ta hannun Ma’aikatar Shari’ar Amurka, sun ƙi goyon bayan neman fitar da bayanan da ba a cire wasu gaɓoɓi ba a matakai da dalilan shari’a da dama.

By Babaji

Leave a Reply