FIFA ta ƙi amincewa da kwamitin riƙon ƙwarya na NFF

Spread the love

Sabbin bayanai sun nuna cewa Hukumar Kula da ƙwallon ƙafa ta Duniya (FIFA) ba ta amince da kafa kwamitin riƙon ƙwarya da aka gabatar domin tafiyar da harkokin Hukumar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya (NFF) ba.

Haka kuma, FIFA ba ta amince da sunayen mambobin da za su kasance cikin irin wannan kwamiti ba, kamar yadda wasu majiyoyi masu inganci da ke da masaniya kan lamarin suka tabbatar.

Majiyoyin sun ce a wani taro da jami’an FIFA suka gudanar da wakilan Gwamnatin Nijeriya da Hukumar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya a birnin Zurich na ƙasar Switzerland, hukumar ta FIFA ta saurari bayanai da matsayoyin da tawagar Nijeriya ta gabatar ne kawai, ba tare da amincewa da kafa kwamitin riƙon ƙwarya nan take ba.

Wata majiya mai inganci ta ce maimakon FIFA ta amince da kafa gwamnatin riƙon ƙwarya nan take, ta yanke shawarar tura tawaga zuwa Nijeriya domin gudanar da bincike kai tsaye kan halin da ake ciki tare da tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harkar ƙwallon ƙafa.

Ta ce ana sa ran ziyarar tawagar FIFA za ta taimaka wa hukumar wajen samun cikakken fahimtar yanayin da ya jawo rikicin da ke ci gaba da faruwa a cikin NFF, musamman bayan da mambobin Kwamitin Zartarwa na NFF ƙarƙashin jagorancin Ibrahim Gusau suka yi murabus gaba ɗaya.

Majiyar ta ƙara da cewa bayan kammala bincike da tuntuɓar masu ruwa da tsaki a Nijeriya, ana sa ran FIFA za ta yi aiki tare da ɓangarorin da abin ya shafa domin samar da taswirar yadda za a kawo ƙarshen rikicin tare da dawo da daidaito da kwanciyar hankali a tafiyar da harkokin NFF.

Ta jaddada cewa FIFA, a matsayinta na babbar hukumar da ke kula da harkar ƙwallon ƙafa ta duniya, tana gudanar da ayyukanta ne bisa ƙa’idoji da dokoki da aka tanada a cikin kundinta da sauran dokokin da suka shafi tafiyar da ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na ƙasashe mambobi.

“Saboda haka, duk wani batu da ya shafi gudanarwa da shugabancin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na ƙasashe mambobi, ana sa ran za a warware shi ne bisa ƙa’idoji da tsarin da FIFA ta tanada.

“Don haka, duk wani mataki da za a ɗauka domin warware halin da ake ciki a NFF dole ne ya yi daidai da kundin dokokin FIFA, ƙa’idojinta da tsarin tafiyar da shugabanci da hukumar ta amince da shi,” inji majiyar.

Majiyar ta kuma yi gargaɗin cewa rahotannin da ke cewa FIFA ta riga ta amince ko ta tabbatar da kafa kwamitin riƙon ƙwarya na NFF, har ma da sunayen mambobinsa, sun yi wuri kuma ya kamata a yi taka-tsantsan da su.

Ta ce, ana sa ran samun ƙarin ci gaba bayan ziyarar da tawagar FIFA za ta kai Nijeriya da kuma tattaunawar da za ta yi da masu ruwa da tsaki kan harkar ƙwallon ƙafar ƙasar.

By ukarofi

Leave a Reply