2027: Idan na ci zaɓe zan dawo wa da ƙananan hukumomi kuɗaɗen su kai tsaye – Atiku 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyyar ADC a zaɓen 2027, Atiku Abubakar, ya yi alkawarin aiwatar da hukuncin Kotun ƙoli kan ‘yancin cin gashin kan ƙananan hukumomi idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa.

A ranar 11 ga Yuli, 2024, Kotun Koli ta yanke hukuncin cewa ya kamata a rika biyan kudaden da ake warewa kananan hukumomi 774 daga Asusun Tarayya kai tsaye zuwa gare su.

Hukuncin ya biyo bayan karar da Gwamnatin Tarayya ta shigar kan gwamnonin jihohi 36 game da yadda ake gudanar da harkokin kananan hukumomi, da kudadensu da kuma ‘yancin cin gashin kansu ta fuskar kudi.

Sai dai duk da wannan hukunci, wasu jihohi har yanzu ba su cika bin umarnin kotun ba.

Sai dai Atiku ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar da cewa kudaden da ake ware wa kananan hukumomi 774 daga Asusun Tarayya (Federation Account) ana tura su kai tsaye zuwa gare su, maimakon a bi ta hannun gwamnatocin jihohi.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Kenneth Okonkwo, ya fitar a jiya Talata, inda ya ce tsohon mataimakin shugaban kasar zai mutunta bin doka tare da karfafa ‘yancin kudi da na gudanar da harkokin kananan hukumomi.

Atiku ya ce idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa, zai tabbatar da cikakken bin hukuncin kotun tare da amfani da ‘yancin cin gashin kan kananan hukumomi wajen bunkasa ci gaba a matakin kasa.

Sanarwar ta ruwaito Atiku yana cewa: “Gwamnatina za ta mutunta hukuncin kotu, ta kare ‘yancin kananan hukumomi, ta tabbatar da cewa kudaden al’umma sun isa ga mutanen da aka ware musu, tare da dawo da sahihin tsarin tarayya.”

A cewarsa, ba wa kananan hukumomi damar samun kudadensu kai tsaye zai ba su damar aiwatar da ayyukan ci gaba da samar da ayyukan more rayuwa cikin inganci, tare da kusantar da mulki ga ‘yan Nijeriya a matakin kasa.

Ya kuma ce kara wa kananan hukumomi ‘yancin cin gashin kansu ta fuskar kudi zai karfafa ikonsu na tunkarar matsalolin tsaro, tare da taimakawa wajen rage talauci.

By ukarofi

Leave a Reply