Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya ce zai kasance mutum na farko daga cikin manyan ’yan adawa da za a fara farauta idan Shugaba Bola Tinubu ya faɗi zaɓen shugaban ƙasa na 2027 a hannun Atiku Abubakar ko Peter Obi.
Wike, wanda ɗan jam’iyyar PDP, ya bayyana goyon bayansa sake zaɓen Tinubu, duk da cewa ba jam’iyyarsu ɗaya ba.
Da yake magana yayin wata tattaunawa da manema labarai, Wike ya ce yana sane da irin sakamakon ka iya zuwa saboda rawar da ya taka, amma hakan ba zai sa ya daina goyon bayan Tinubu ba.
“Ni ne ɗan siyasa na farko da za a fara farauta. Ni ne na farko. Na san za su zo ta kaina,” in ji shi.
Tsohon gwamnan Jihar Ribas ya ce duk da akwai yiwuwar ya fuskanci matsala, amma hakan ba zai hana shi goyon bayan yaƙin neman zaɓen Tinubu ba.
“Duk ranar da na kwanta barci, ina tunanin sake zaɓen shugaban ƙasa. Idan ina cin abinci, ina tunanin sake zaɓensa. Duk abin da nake yi yanzu ya shafi sake zaɓen shugaban ƙasa ne,” in ji shi.
Wike, ya kuma ce ya fuskanci ƙalubale a siyasa saboda matsayar da ya bi, amma ya jaddada cewa ba ya damuwa da kalaman masu sukarsa.
“Ban ga wani mutum a ƙasar nan da aka tsana kamar ni ba. Amma ban damu da abin da mutane suke faɗa ba. Abin da ya dame ni shi ne, kamar yadda na faɗa, zan goyi bayan Shugaban ƙasa,” inji shi.
Goyon bayan Wike ke yi wa Tinubu ya haifar da rashin jituwa a cikin PDP, musamman yayin da jam’iyyun adawa ke ƙoƙarin haɗa ƙarfi waje ɗaya domin tunkarar zaɓen 2027.
Atiku da Obi, waɗanda suka fafata a zaɓen shugaban ƙasa na 2023 ƙarƙashin PDP da LP, ana hasashen za su yi haɗin gwiwa domin kayar da Shugaba Tinubu.
Wike, ya ce ya fahimci cewa rashin nasarar Tinubu na iya jefa sanya shi ya fuskanci ƙalubale daga abokan hamayya, amma ya ce hakan ba zai sauya matsayinsa na goyon bayan shugaban ƙasa ba.
