An ba Gwamnan Zamfara lambar yabo ta Gwarzon Gwamna a bikin cikar jaridar DAILY TIMES shekara 100

Spread the love

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya karɓi lambar yabo ta Gwarzon Gwamna na Yankin Arewa maso Yamma da jaridar DAILY TIMES ta ba shi, a yayin bikin cika shekaru 100 da kafuwar jaridar wanda aka gudanar a Abuja.

An ba gwamnan lambar yabon ne a ranar Alhamis, 3 ga Satumba, 2026 a wajen bikin “DTN@100 Times Heroes Awards”, wanda DAILY TIMES, wadda ake yi wa kallon jarida mafi daɗewa a Nijeriya, ta shirya domin murnar cika shekaru 100 da kafuwarta.

A sanarwar da Kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya ce an karrama Gwamna Lawal ne bisa la’akari da irin jagorancinsa, hidimar da yake yi wa jama’a da kuma gudunmawar da yake bayarwa wajen ci-gaban ƙasa.

Lambar yabon na daga cikin shirye-shiryen bikin cika shekaru 100 na jaridar, wadda aka fara wallafawa a shekarar 1926, kuma ta kasance tana bibiyar sauye-sauyen siyasa, tattalin arziƙi, zamantakewa da al’adun Nijeriya a tsawon ƙarni guda.

Shugaban Majalisar Kyaututtukan Jaruman DTN@100, Bolaji Okusaga, ya bayyana cewa an zaɓi Gwamna Lawal ne bayan ya samu mafi yawan ƙuri’u da sunayen waɗanda aka gabatar a matsayin ’yan takara a yankin Arewa maso Yamma.

Okusaga ya ce, bayan gudanar da cikakken tsarin gabatar da sunayen ’yan takara da kuma kaɗa ƙuri’ar jama’a, Gwamna Lawal ne ya samu mafi yawan ƙuri’u a wannan rukuni.

Ya ƙara da cewa, Majalisar Kyaututtukan Jaruman Times da sauran masu ruwa da tsaki sun tabbatar da zaɓensa, bisa la’akari da jagorancinsa, hidimar jama’a da gudunmawar da yake bayarwa wajen ci gaban Nijeriya.

Da yake karɓar kyautar, Gwamna Lawal ya nuna godiyarsa ga Kwamitin Daraktoci, Hukumar Gudanarwa da Kwamitin Shirya Bikin Cika Shekaru 100 na Daily Times Nigeria, da kuma Majalisar Kyaututtukan Jaruman Times da dukkan ’yan Nujeriya da suka mara wa takararsa baya.

Gwamnan ya ce karramawar ta ƙara tabbatar da jajircewarsa wajen inganta shugabanci nagari da samar da ingantaccen aikin gwamnati ga al’ummar Jihar Zamfara.

Daga cikin sauran fitattun ’yan Nijeriya da aka karrama a wajen taron akwai Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Sanata George Akume, da tsohon Shugaban Bankin Raya Afirka (AfDB), Dakta Akinwumi Adesina.

Jaridar ta sanar da cewa za a saka sunayen mutanen da cibiyoyin da suka samu kyaututtukan DTN@100 Times Heroes Awards cikin jerin fitattun mutane da cibiyoyin da suka taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban Nijeriya a cikin wani babban littafi mai shafuka 700 mai suna Nigerian Grand Book.

A cewar jaridar, littafin zai kasance kundin tunawa da ƙasa baki ɗaya, tare da zama madogara ta tarihi da za ta adana tarihin mutane, cibiyoyi da nasarorin da suka taimaka wajen tsara tafiyar da lamuran ci-gaba a Nijeriya. Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya rubuta gabatarwar littafin “Nigerian Grand Book”.

By Babaji

Leave a Reply