
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mai Martaba Sarkin Masarautar Gumel a Jihar Jigawa, Alhaji Dakta Ahmed Muhammad Sani na II, CON ya rasu.
Basaraken ya rasu ne a ranar Alhamis a Misra, lamarin da ya jefa al’ummar Gumel da Jihar Jigawa cikin jimami, inda ake tsammanin gaisuwar ta’aziyya daga sassan jihar da ma wajenta.
Wannan al’amari babban rashi ne ga iyalansa, abokan arziƙi da ilahirin yankin Gumel, yayin da aka yi addu’ar Allah ya jiƙan sa ya gafarta masa kurakuransa, sannan ya sanya shi a gidan aljanna. Haka kuma, an yi addu’ar Allah ya bai wa makusanta da ‘yan Gumel haƙurin juriyan rashin sa.
Rasuwar basaraken na wakiltar gagarumar rashi ga Masarautar Gumel ganin yadda cibiyoyin sarautar gargajiya suke taka muhimmiyar rawa wajen ci-gaban zaman lafiya, haɗin kai, martabobin al’ada da inganta yankuna.
Masarautar Gumel ɗaya ce daga cikin masarautun arewacin Nijeriya da suke da daɗaɗɗen tarihi da tasiri acikin zamantakewa da al’adun al’ummarta.
