Sojoji sun ceto matar janar bayan musayar wuta da ‘yan bindiga a Abuja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar Sojojin Nijeriya ta ce ta yi nasarar ceto matar wani birgediya janar mai ritaya da aka sace ta daga gidanta da ke Abuja a ranar 1 ga Satumba, 2026, bayan dakarun tsaro sun yi musayar wuta da ‘yan bindiga.

Rahotanni sun ce bayan garkuwar, sojojin rukunin Guards Brigade and Army Headquarters (AHQ) Garrison ne suka ƙaddamar da atisayen ceton a yankunan da ‘yan bindigar suke tserewa, inda suka gano su tare da ceto matar. Yayin da suka samu bayanan sirri, dakarun sun kutsa ta yankin rukunin gidajen Aco Estate zuwa ƙauyen Goza, inda suka yi arangama da masu garkuwar.

Kasancewar dakarun tsaron sun nuna fin ƙarfin makamai kan masu laifin, hakan ya sa suka ja da bayan tare da barin matar da tserewa zuwa bayan gari, lamarin da ya sa aka ceto ta a yankin ƙauyen Angwan Sabo.

Daga nan ne sojojin suka faɗaɗa atisayen nasu a yankin Aco Estate zuwa Angwan Sayawa wajen tura ƙarin dakaru domin tare wuraren da ake zaton ‘yan bindigar za su bi su tsere.

A wani atisayen a ranar 2 ga Satumba, 2026 sojojin sun kama mutum biyu da ake zargi da hannu a garkuwar a kusa da ƙauyen Gaube a Ƙaramar Hukumar Kuje da ke Babban Birnin Tarayyar. Haka kuma, sojojin sun ƙwato bindiga ƙirar AK-47, kwanson alburusan AK-47 da alburusan 7.62mm guda 19, yayin da suke cigaba da ƙoƙarin kamo sauran ‘yan bindigar.

Kazalika, rundunar ta kuma yaba wa al’umma bisa sanya ido da bayar da haɗin kai, tana mai jaddada aniyarta ta cigaba da bai wa rayuka da dukiyoyinsu kariya tare da haɗin-gwiwar sauran hukumomin tsaro a Abuja da kewayenta.

By Babaji

Leave a Reply