Ladabinka ta ƙarfafa kyawawan manufofin Tinubu, inji Iliyasu Kwankwaso ga Shettima yayin zagayowar ranar haihuwarsa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Yayin da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima ke cika shekaru 60 a duniya, an bayyana shi a matsayin mutum mai ban mamaki wanda haƙuri, kiyaye amana da kuma ƙaunarsa ga shugabancin ƙasarsa suka bayar da gudummawa wajen ci-gaban Ajandar Sabon Fata ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin ingantacciyar Nijeriya.

Alhaji Musa Illiyasu Kwankwaso, Darakta Zartarwa na Harkokin Kuɗi na Hukumar kula da Kogunan Haɗejia da Jama’are ne ya bayyana haka yayin taya Mataimakin Shugaban Ƙasar murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

Ya ce: “A yau Najeriya ta fi samun ƙarfafa alaƙa tsakanin ƙabilu daban-daban, saboda haɗin-gwiwar dabaru da ke tsakanin Sanata Shettima da shugabansa wanda ya murkushe tunanin wasu da ke son tayar da rikici tsakaninsu.

“Mataimakin Shugaban Ƙasa, haɗin-gwiwar dabaru da kuka yi tare da Mai Girma Shugaba Bola Ahmed Tinubu, GCFR, ya kasance ginshiƙi wajen cigaba da Tsarin Sabunta Fata da kuma aiwatar da sauye-sauyen da za su kawo sauyi mai amfani,” inji shi.

Ya ƙara da cewa: “Fahimtar siyasarku, ƙwarewa da kuma iyawar ku ta haɗa kan jama’a sun ƙara ƙarfafa gwamnati wajen bin tsarin ci-gaba mai ɗorewa, tare da samar da haɗin kai tsakanin ƙabilun ƙasa.”

Ya ci gaba da cewa: “Yayin da kake cika shekaru 60 a yau, na haɗa muryata da na iyalinku, abokan arziƙi da miliyoyin ‘yan Nijeriya wajen taya ka murna. Kai fitaccen ɗan siyasa ne kuma ɗan ƙasa mai kishin ƙasa wanda tarihin hidimar sa ga jama’a ya nuna jarumta, tawali’u, zurfin tunani da jajircewa wajen ganin an samu ci-gaban Nijeriya.”

“Baya ga harkokin gwamnati, gudummawar da ka bayar wajen haɗin kai da dorewar babbar jam’iyyar mu, All Progressives Congress (APC), na nuna cewa kai jagora ne mai hangen nesa da ke son ganin an ƙarfafa cibiyoyin dimokuraɗiyya.”

“A gare mu, wajibcin mu shi ne ci gaba da ba ku goyon baya da goyon bayan gwamnati domin tabbatar da zaman lafiya, wadata da cigaban ƙasa.”

A ƙarshe, ya ce a matsayinsa na shugaba mai ba da ƙwarin-gwiw, mutane kamar sa za su cigaba da koyi da nagartattun halayensa tare da yin addu’a don samun nasarar sa da ta Shugaba Tinubu.

By Babaji

Leave a Reply