Daga JAMIL GULMA a Kebbi
A cikin shirin sa na tallafa wa masu ƙananan sana’o’i a ƙaramar hukumar Augie, kwamishinan lafiya na jihar Kebbi Honarabul Sama’ila Muhammed Augie ya raba Naira milliyan 14 a matsayin tallafi ga masu ƙananan sana’o’i.
Da ya ke jawabi lokacin ƙaddamar da gudunmawar a garin Augie da kuma Bubuche kwamishinan ya ce wannan tallafi ne na masu ƙananan sana’o’i don ƙara samun jari.
Ya bayyana cewa wannan yana ɗaya daga cikin shirye-shiryen da ke gaban sa na ganin al’umma sun tashi tsaye don neman na kansu a maimakon yawon maula.
Yanzu lokaci na zaman banza ya wuce yana da kyau kowa ya nemi abin yi kuma kada a raina sana’a duk yadda ta ke.
Ɗaya daga cikin waɗanda suka ci gajiyar wannan shirin Malam Sarkin Fawa Mera ya yaba wa kwamishinan musamman bisa ga yadda ya tsara tallafin na ɗauko mutane daga kowace mazaɓa a cikin ƙaramar hukumar Augie inda ya zaƙulo waɗanda ke ƙananan sana’o’i, inda ya nemi yan siyasa da su yi koyi da shi saboda idan manyan yan siyasa suna yin irin haka in sha Allahu nan gaba har masu manyan sana’o’i za su shigo.
