
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ICPC, ta kori wani jami’inta mai suna Daniel Stephen, bisa zargin sa da shigar da Aichatou Asabe El-Rufa’i, wato ɗaya daga cikin matan tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai cikin farfajiyarta ba bisa doka ba domin ganin mijinta da ke tsare.
Rahotanni sun bayyana cewa, an gano haka ne ta kyamarorin tsaro, inda aka ga Stephen yana taimaka wa Aichatou Asabe El-Rufa’i shiga yankin farfajiyar hukumar ta wajen da aka haramta wa baƙi zuwa. A cewar wani rubutun Stephen da wannan jarida ta gani, al’amarin ya faru ne a ranar 5 ga Yuli, 2026, yayin da aka haɗa jami’in aiki da tawagar tsaron cikin gida na ICPC.
Tsohon gwamnan na fuskantar shari’ar zargin satar kuɗaɗe da sauya akalar wasu kadarorin al’umma, kuma ya kasance a tsare tun a ranar 19 ga Fabrairu, bayan Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati EFCC ta sako shi. ICPC ta cigaba da bincike da gurfanar da shi kan zarge-zargen da suka shafi rashawa.
A sanarwar da ya miƙa wa kwamitin bincike, Stephen ya tabbatar da cewa ya taimaka wa matar El-Rufa’in wajen sun damar zuwa wajen da aka tsare mijin nata “ta ƙofar baya”.
A cewar majiyoyin ICPC, Stephen ya tuƙa matar ne zuwa cikin farfajiyar hukumar, sannan ya jagorance ta ta ƙofar shiga ta baya ya kuma raka ta zuwa sashen bene inda a nan ne aka ajiye El-Rufa’i. A rubutun nasa, ya nuna cewa sai da ya kashe wutar lantarkin yankin kafin ya kai matar zuwa ɗakin da El-Rufa’i yake. Stephen ya ce ya fitar da ita ne ta ƙofar da suka shiga bayan ganawar mintina 15 da mijin nata kan batun shari’a, yana mai amsa cewa ya yi laifi wajen saɓa doka kan al’amarin.
A watan Agusta ne dai El-Rufa’i ya shigar da ƙarar ICPC na neman a biya shi diyyar Naira biliyan 10 kan zargin hana mata da ɗansa ganin sa yayin da yake tsare a komar hukumar, lamarin da ya haifar da sabon rikicin shari’a tsakanin tsohon gwamnan da ICPC.
