Alhaji Ahmad Muhammad Sani: Sarkin Gumel ya rasu bayan shekaru 45 a karaga

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Rasuwar Sarkin Gumel, Alhaji Dakta Ahmad Muhammad Sani II, ta rufe wani babban shafi na tarihin sarautar gargajiya a Arewacin Nijeriya; shafi ne da ya ɗauki sama da shekaru 45 ana rubutawa da ilimi, gogewa, siyasa, shugabanci da ƙoƙarin daidaita al’ada da zamani.

Marigayin ya rasu ne a ranar Alhamis, 3 ga Satumba, 2026, a ƙasar Masar, yana da shekaru 83 a duniya. Rasuwarsa ta jefa Masarautar Gumel da Jihar Jigawa cikin jimami, yayin da ake ci gaba da miƙa saƙonnin ta’aziyya daga gwamnati, sarakuna, ’yan siyasa, shugabannin al’umma da sauran jama’a. 

Amma kafin rasuwarsa, Ahmad Muhammad Sani II ya riga ya kafa tarihi a matsayin ɗaya daga cikin sarakunan da suka daɗe suna kan karagar mulki a Nijeriya. A ranar 16 ga Disamba, 2020, ya cika shekaru 40 kan gadon sarautar Gumel, bayan da aka zaɓe shi ya gaji mahaifinsa da ya rasu a ranar 13 ga Disamba, 1980. 

Tarihin rayuwarsa kuwa bai fara ne a cikin fadar sarauta ba. Ya fara ne da neman ilimi, aikin gwamnati, siyasa da hidimar jama’a, kafin daga bisani ƙaddara ta mayar da shi cikin fadar da ya fito.

ɗan sarauta mai son ilimi:

An haifi Ahmad Muhammad Sani II a ranar 12 ga Disamba, 1942.

Ya fara karatun firamare a Makarantar Firamare ta Gumel daga shekarar 1948 zuwa 1953. Daga nan ya wuce Makarantar Tsakiya ta Hadejia, inda ya yi karatu daga 1953 zuwa 1956.

Bayan haka ya koma Kano domin karatun sakandare a Kano High School da ke Kwalejin Rumfa, inda ya kammala karatunsa a shekarar 1961. 

A lokacin da zuwa makaranta ba abu ne da ya zama ruwan dare ga yara da dama a Arewacin Nijeriya ba, marigayin ya samu damar ci gaba da karatu, abin da daga baya ya zama ɗaya daga cikin abubuwan da suka bambanta salon shugabancinsa.

A wata hira da Trust Radio a 2020, ya tuna cewa a lokacin ƙuruciyarsa wasu yara da ke zuwa makaranta ba su da abin da za su ci. Ya ce kakarsa kan dafa abinci da sassafe, sannan ta yi fura domin sayarwa, yayin da yara da dama ke zuwa gidanta su ci abin da ya rage ba tare da biyan kuɗi ba kafin su wuce makaranta. 

Wannan ƙwarewar rayuwa ta farko ta zama wani ɓangare na fahimtarsa kan matsalolin talakawa da kuma muhimmancin ilimi.

Karatu ya kai shi Zariya da Amurka:

Bayan kammala karatun sakandare, Ahmad Muhammad Sani II ya shiga Cibiyar Gudanar da Ayyukan Gwamnati da ke Zariya, wadda daga baya ta kasance cikin tsarin Jami’ar Ahmadu Bello, inda ya samu Diploma a fannin Gudanar da Harkokin Jama’a a shekarar 1963.

Daga baya ya koma makarantar domin ƙara samun Babban Diploma a wannan fanni a shekarar 1970.

A shekarar 1972 kuma ya tafi Jami’ar Ohio da ke Athens, Ohio, a Amurka, inda ya yi karatun Kimiyyar Siyasa da kuma Hulɗar ƙasa da ƙasa, ya kammala karatunsa a shekarar 1978. 

A wata hira da ya yi da Trust Radio, ya tuna cewa wani ɗan uwansa, wanda daga baya ya zama Wazirin Gumel, shi ne ya riga shi zuwa Amurka da shekara guda, kuma ya taimaka masa wajen samun gurbin karatu a Jami’ar Ohio.

Sun zauna a gida ɗaya, suna amfani da abin hawa guda wajen harkokinsu. Marigayin ya kuma tuna yadda ya sayi wata mota ƙirar Mustang Sport da suke amfani da ita wajen zirga-zirga a ƙarshen mako.

A cewarsa, kasancewar ɗan uwansa ya riga shi zuwa Amurka ya sauƙaƙa masa rayuwa, har ya ji kamar yana rayuwa ne a Gumel duk da cewa yana wata ƙasa mai nisa. 

Daga aikin gwamnati zuwa siyasa:

Kafin ya shiga siyasa, Sani II ya fara aiki da Hukumar Kula da Harkokin Gumel ta Gargajiya (Gumel Natiɓe Authority) daga 1961 zuwa 1963.

A shekarar 1964 ya shiga Sashen Shige da Fice, inda aka tura shi Ngamboru Ngala a Jihar Borno. Daga baya, a shekarar 1972, aka naɗa shi babban jami’in gwamnati a ofishin yankin Kazaure. 

Sai dai babban sauyin rayuwarsa ya zo ne a shekarar 1978, lokacin da ya shiga siyasa. Ya tsaya takarar kujerar Majalisar Dattawa a ƙarƙashin Babbar Jam’iyyar Jama’ar Nijeriya (GNPP), ko da yake bai samu nasara a zaɓen ba.

Daga baya, haɗin gwiwar GNPP da Jam’iyyar Ceton Jama’a (PRP) ya buɗe masa ƙofa zuwa gwamnatin Jihar Kano, inda aka naɗa shi Kwamishinan Yaɗa Labarai, Harkokin Cikin Gida da Al’adu.

Ya riƙe muƙamin daga 1978 zuwa 1980. A lokacin aikinsa, ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa da bunƙasa kafafen yaɗa labaran gwamnatin Jihar Kano, ciki har da jaridar Triumph da tashar talabijin ta CTɓ67, wadda daga baya aka fi sani da ARTɓ, tare da faɗaɗa aikin Rediyon Kano. 

Wannan ya sanya shi cikin mutanen da suka taka rawa a farkon ci gaban kafafen yaɗa labaran gwamnati a tsohuwar Jihar Kano.

Sarauta ta katse masa siyasa:

A lokacin da yake ƙoƙarin gina makomarsa a siyasa, rayuwarsa ta sake sauyawa kwatsam. A ranar 13 ga Disamba, 1980, mahaifinsa, Sarkin Gumel mai ci a lokacin, Alhaji Muhammad Sani II, ya rasu.

Kwana uku kacal bayan haka, a ranar 16 ga Disamba, 1980, aka zaɓi Ahmad Muhammad Sani II ya gaji mahaifinsa a matsayin Sarkin Gumel. Ya kasance matashi mai shekaru sama da 30 a lokacin.  Ta haka ne aka katse masa harkar siyasa, aka mayar da shi cikin fadar sarautar da ta zama sabon filin hidimarsa ga al’umma.

Gwamnatin Jihar Jigawa ta bayyana shi a matsayin Sarki na 16 na Masarautar Gumel, kuma ta ce ya kasance kan karagar mulki tun daga 1981. 

Sarkin da ya buɗe ƙofar fadar sa ga jama’a:

ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi bayyana salon mulkin marigayin shi ne abin da shi kansa ya kira “Open-Door Policy”, wato tsarin buɗe ƙofa ga jama’a.

A hirar da ya yi a shekarar 2020, ya ce lokacin da ya hau sarauta ya kawo sauye-sauye da dama, ciki har da barin talakawansa su riƙa zuwa gare shi kai tsaye domin gabatar da ƙorafe-ƙorafensu. Ya ce mutane sun yi mamakin wannan salon saboda ba su saba ganin sarki yana buɗe ƙofarsa ga kowa domin sauraron matsalolinsu kai tsaye ba.

“Mutane suna da ’yancin zuwa su yi tambaya kan komai,” ya bayyana, yana mai cewa batutuwan sun haɗa da ci gaba, noma da kasuwanci. 

A cewarsa, iliminsa da gogewarsa a aikin gwamnati sun taimaka wajen fahimtar cewa akwai buƙatar a haɗa al’ada da wasu hanyoyin gudanar da shugabanci na zamani.

Sarauta tsakanin al’ada da zamani:

Sarkin ya bayyana kansa a matsayin basaraken da yake son kawo zamani cikin tafiyar da masarauta, ba tare da watsar da al’adun da suka gada daga kakanni ba. Wannan matsaya ta zama ginshiƙin salon mulkinsa na tsawon shekaru. Ya kuma yi amfani da matsayinsa wajen ƙarfafa jama’a su rungumi ilimi, musamman ilimin zamani.

A cewarsa, a matsayinsa na ɗan sarauta, ya ga cewa ya zama abin koyi ga iyalan da ke hana ’ya’yansu zuwa makaranta.

Ya ce ya kan kira wasu iyaye ya shawarce su da su bar ’ya’yansu su nemi ilimi, yana tunatar da su cewa idan shi ɗan sarauta ya iya barin gida ya tafi wata ƙasa mai nisa mai bambancin harshe da al’adu domin neman ilimi, to babu dalilin da zai sa sauran iyaye su hana ’ya’yansu yin hakan.

Ya ce hakan ya sa wasu suka fara ganin cewa idan ɗan sarki ya iya zuwa ƙasar waje neman ilimi, to su ma za su iya tura ’ya’yansu makaranta. 

Sarauta a matsayin hidima:

A yayin da shekarun mulkinsa suka ƙaru, marigayin ya ƙara mai da hankali kan matsalolin jama’a. Ya shaida cewa lokaci mai yawa yana ƙarewa ne wajen sauraron ƙorafe-ƙorafen talakawansa da yanke hukunci kan matsalolin da suke gabatarwa. Ya kuma bayyana cewa wani lokaci yana ba mutane wasiƙun gabatarwa daga ofishinsa, waɗanda suka taimaka wa wasu samun damar zama wakilan wasu kayayyaki a Gumel.

A cewarsa, wasu daga cikin waɗanda ya taimaka wa kan dawo su yi masa godiya, abin da yake kallonsa a matsayin wani ɓangare na dalilin da ya sa yake kan karagar sarauta. 

Shawarwarin sa ga al’umma:

Shawarwarin marigayin ga al’ummar Gumel ba su tsaya kan siyasa ko tsaro ba. Ya yi kira ga mutanen masarautar su rungumi sauye-sauyen zamani, musamman a fannonin ilimi, noma, aikin gona da inganta rayuwar jama’a. Ya kuma nuna damuwa kan yadda ake zubar da shara da gawawwakin dabbobi a wuraren da bai dace ba, yana mai cewa hakan na iya jawo cututtuka.

A cewarsa, ya yi ƙoƙari wajen wayar da kan jama’a kan buƙatar tsaftar muhalli da kuma guje wa abubuwan da za su iya jefa lafiyar al’umma cikin haɗari. 

Sarautar da ta daɗe fiye da shekaru 45:

A tsawon mulkinsa, Ahmad Muhammad Sani II ya zama ɗaya daga cikin sarakunan da suka fi daɗewa kan karagar sarauta a Nijeriya. A shekarar 2020, lokacin da ya cika shekaru 40 a kan gadon sarauta, ya ce ya ji daɗin kasancewarsa a kan karagar tun daga ranar da aka zaɓe shi, yana mai cewa ya kawo sauye-sauye masu yawa a yadda ake gudanar da harkokin masarautar. 

Yanzu, bayan rasuwarsa a shekarar 2026, mulkin da ya ɗauki sama da shekaru 45 ya zo ƙarshe.

Ya bar tarihi mai cike da haɗuwar fannoni daban-daban: ɗan sarauta mai neman ilimi, ma’aikacin gwamnati, ɗan siyasa, kwamishina, kuma daga ƙarshe basaraken da ya shafe fiye da shekaru arba’in yana jagorantar Masarautar Gumel.

Gumel ta rasa jagora:

Rasuwar Sarkin ta zo ne a lokacin da Masarautar Gumel ke ci gaba da riƙe matsayinta na ɗaya daga cikin tsoffin cibiyoyin gargajiya na Arewacin Nijeriya.

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga Jihar Jigawa, masarautar gargajiya da al’ummar Gumel, yana mai bayyana marigayin a matsayin basaraken da ya sadaukar da rayuwarsa wajen zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban jama’arsa. 

A yanzu, abin da ya rage shi ne tarihin da ya bari — tarihin wani basarake da ya hau gadon sarauta yana matashi, ya shafe shekaru da dama yana jagorantar jama’a, kuma ya yi ƙoƙarin haɗa abin da ya gada daga kakanni da abubuwan da zamani ya zo da su.

Ga al’ummar Gumel, rasuwar Ahmad Muhammad Sani II ba wai ƙarshen rayuwar mutum ɗaya ba ce kawai; ita ce ƙarshen wani dogon zamani a tarihin masarautar.

Allah Ya jiƙan sa da rahama, Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya sa Aljannatul Firdausi ce makomarsa, Ya kuma bai wa iyalansa da al’ummar Gumel da Jihar Jigawa haƙurin jure wannan babban rashi.

By ukarofi

Leave a Reply