Bincikenmu kan Tinubu ba ya nufin ya aikata laifi – FBI

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta ƙasar Amurka (FBI) ta tabbatar da cewa, Shugaban ƙasar Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya taɓa kasancewa cikin mutanen da aka gudanar da binciken laifi akansu da ya shafi safarar miyagun ƙwayoyi a farkon shekarun 1990, sai dai hukumar ta jaddada cewa, wannan bayani ba ya tabbatar da cewa, ya aikata wani laifi.

Hukumar FBI ta bayyana hakan ne a wata takardar rantsuwa da ta gabatar mai kwanan watan 28 ga Agusta, 2026, a gaban Kotun Gundumar Amurka ta District of Columbia, a cikin wata shari’a da ake yi ƙarƙashin Dokar ’Yancin Samun Bayanai ta Amurka (FOIA), wadda ke neman samun bayanan da suka shafi Shugaban ƙasar Nijeriya.

A cewar takardar, bayanan da ake nema an tattara su ne a yayin binciken da FBI ke gudanarwa kan wasu mutane da ake zargi da aikata laifukan safarar miyagun ƙwayoyi.

Hukumar ta kuma amince cewa kotun ta riga ta tabbatar da cewa an samu sanarwar hukuma game da wani bincike da ya shafi Tinubu.

Wannan sabon ci gaba ya biyo bayan hukuncin da Alƙalin Kotun Gundumar Amurka, Beryl Howell, ta yanke a watan Afrilun 2025, inda ta ce FBI da Hukumar Yaƙi da Safarar Miyagun ƙwayoyi ta Amurka (DEA) ba za su ci gaba da amfani da abin da ake kira “Glomar response” wajen ƙin tabbatarwa ko musanta kasancewar bayanan da suka shafi Tinubu ba.

Alƙali Howell ta ce, hukumomin biyu sun gaza gabatar da isassun dalilan da suka shafi kare sirrin mutum da za su ba su damar ɓoye cewa an taɓa gudanar da binciken laifi kan Tinubu. Saboda haka, ta umarci hukumomin su sarrafa bayanan da ba su cikin bayanan da dokar FOIA ta keɓe daga bayyanawa. Sai dai hukuncin kotun bai tabbatar da cewa Tinubu ya aikata laifin safarar miyagun ƙwayoyi ba, kuma bai nuna cewa an taɓa yanke masa hukunci kan wani laifi ba.

Shari’ar FOIA ta samo asali ne daga buƙatun da wani Ba’amurke mai fafutukar neman gaskiya da buɗaɗɗen bayanai, Aaron Greenspan, ya shigar. Daga cikin bayanan da ya nema akwai cikakken fayil ɗin FBI kan Bola Ahmed Tinubu da kuma bayanan tambayoyin da jami’an hukumar suka gudanar da shi, waɗanda aka rubuta a Form 302, ƙarƙashin lambar shari’a ta FBI 245-IP-71386-UUUUUU tsakanin shekarun 1992 zuwa 1993.

Buƙatun suna da alaƙa da wani babban yunƙuri na samun bayanan da suka shafi wata hanyar safarar hodar heroin da aka gudanar daga birnin Chicago, wadda hukumomin Amurka suka gudanar da bincike a kanta a farkon shekarun 1990.

Sai dai FBI ta ci gaba da riƙe wasu sassan bayanan da aka nema, tana mai dogaro da wasu tanade-tanaden dokar ’yancin samun bayanai ta Amurka da suka shafi kare sirrin mutum, bayanan majiyoyin sirri, dabarun gudanar da binciken laifuka da kuma bayanan da bayyanawarsu ka iya jefa wasu mutane cikin haɗari. Hukumar ta ce, ba za ta iya bayyana cikakken dalilin da ya sa ta keɓe wasu daga cikin bayanan ba a bainar jama’a.

Sabon bayanin FBI ya samu yaɗuwa ne ta hannun ɓon Batten-Montague-York, wani kamfanin tuntuba da harkokin siyasa da ke Washington, wanda rahotanni suka ce tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya ɗauka aiki gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027. A cikin wata sanarwa da kamfanin ya wallafa a shafinsa na ɗ, ya ce yana nazarin ɗimbin bayanan da ya samu daga FBI, tare da cire wasu sassa daga bayanan da ake ganin ya dace a ɓoye. Kamfanin ya yi zargin cewa takardar rantsuwar FBI ta ci karo da iƙirarin cewa Tinubu bai taɓa kasancewa wanda ake gudanar da binciken laifi a kansa ba. 

Kamfanin ya ce, “FBI ta bayyana a ƙarƙashin rantsuwa cewa kotu ta riga ta tabbatar da cewa an amince a hukumance da gudanar da binciken laifi kan Shugaban ƙasar Nijeriya, Bola Tinubu.”

Sai dai Fadar Shugaban ƙasa ta mayar da martani mai ƙarfi, inda ta yi watsi da lamarin tare da bayyana shi a matsayin wata dabara ta siyasa. Mai Bai Shugaban ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Sadarwar Jama’a, Sunday Dare, ya zargi Atiku da amfani da kamfanin tuntuɓar siyasar da ke Washington wajen tayar da cece-kuce gabanin zaɓen 2027. Dare ya bayyana lamarin a matsayin “bayyananniyar alamar matsananciyar siyasa”, yana mai cewa fitar da takardar kotun ba wani sabon gagarumin binciken sirri ba ne.

“Yaƙin neman ɗaukar hankalin kafafen yaɗa labarai da aka tsara a Washington, D.C., ba wani sabon gagarumin binciken sirri ba ne; bayyananniyar alamar matsananciyar siyasa ce,” inji Dare. Ya kuma yi gargaɗin cewa bai kamata a ɗauki kalaman da kamfanin tuntubar siyasar ya fitar a matsayin matsayin Gwamnatin Amurka ba. Ya ce, sanarwar da ake fitarwa daga Washington na neman tayar da hankali “takardun farfaganda ne na hulɗa da jama’a da ake gabatarwa tamkar ra’ayin Gwamnatin Amurka, alhali ba haka ba ne.”

Dare ya ƙalubalanci masu yin ƙarin zarge-zarge kan Shugaban ƙasar da su fito da hujjojin da za su tabbatar da ikirarinsu, musamman dangane da wani rahoton leƙen asiri da ake cewa yana da matuƙar sirri.

Ya ce, “Muna buƙatar su fito da abin da suke kira ‘rahoton leƙen asiri mai matuƙar sirri’, su bayyana majiyoyin da ba su ambaci sunayensu ba, sannan su gabatar da hujjoji na zahiri kan zarge-zargen da suke yi.”

Mai bai wa shugaban ƙasar shawarar ya kuma yi zargin cewa takardun da aka shigar ƙarƙashin Dokar Rajistar Wakilan ƙasashen Waje ta Ma’aikatar Shari’a ta Amurka sun nuna cewa Atiku ya ɗauki kamfanin ɓon Batten-Montague-York, L.C. aiki kan kwangilar dala miliyan 1.2 na tsawon watanni 12.

A cewar Dare, an ɗauki kamfanin ne domin ya taimaka wajen “daidaita” labaran da Gwamnatin Nijeriya ke gabatarwa, tare da amfani da tsoffin bayanan shari’o’in Amurka a matsayin makamin siyasa gabanin zaɓen 2027.

Ya kuma yi tambaya kan rawar babban jami’in kamfanin, Dr Karl-Marɗ Edward Okeke-ɓon Batten, a cikin shari’ar FOIA, yana mai cewa kamfanin ba shi da alhakin gudanar da shari’ar da ake yi a kotun.

A nasa ɓangaren, ɗaya daga cikin lauyoyin da ke wakiltar Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a Amurka, Wole Afolabi, Babban Lauyan Nijeriya (SAN), ya yi watsi da zarge-zargen da ake dangantawa shugaban da safarar miyagun ƙwayoyi, yana mai cewa da a ce gwamnatin Amurka na da sahihiyar hujjar da za ta tabbatar da hakan, da tuni ta gurfanar da shugaban a gaban shari’a.

Afolabi ya bayyana hakan ne yayin da yake tattaunawa da gidan talabijin na Channels a shirin Sunday Politics, inda ya yi bayani kan cece-kucen da ya biyo bayan ƙoƙarin samun wasu bayanan bincike da hukumomin tsaron Amurka suka tattara game da Tinubu.

Bayanan sun kasance a tsakiyar wata ƙara da aka shigar ƙarƙashin Dokar ’Yancin Samun Bayanai ta Amurka (Freedom of Information Act), wadda Aaron Greenspan ya shigar a kan gwamnatin Amurka.

Greenspan na neman takardun da Ma’aikatar Shari’a ta Amurka, Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Tarayya (FBI) da Hukumar Yaai da Safarar Miyagun ƙwayoyi ta Amurka (DEA) ke riƙe da su, waɗanda suka shafi binciken da aka taɓa gudanarwa a baya kan Tinubu.

A cewar lauyan, gwamnatin Amurka ta riga ta fitar da dubban shafuka na takardun, sai dai tana ƙin bayyana wasu sassan da aka rufe ko aka goge bayanansu. Afolabi ya ce, ba a yi hakan ne domin kare Tinubu ba, illa dai domin kare majiyoyin bayanan sirri, hanyoyin gudanar da bincike da kuma jami’an tsaro da ke da hannu a binciken.

Da yake magana kan matakin da lauyoyin Tinubu suka ɗauka na shigar da ƙara a Amurka domin ƙalubalantar ci gaba da ɓoye wasu sassan takardun, Afolabi ya ce rashin yin hakan zai kasance tamkar laifin ƙwarewa ne daga ɓangaren lauyoyin. Ya ce, dokar Amurka ce ta bai wa abokan hulɗarsu damar neman kariya daga bayyana wasu bayanai, don haka wajibi ne su yi amfani da wannan dama.

“Abin da Greenspan ke nema shi ne a cire duk wani ɓoyayyen sashe daga takardun kafin a ba shi. Amma tsarin dokar shi ne, ba abin da mutum yake so ake bi ba; abin da doka ta tanada ake bi. Abin da muke yi shi ne amfani da kariyar da doka ta bayar. Idan ba mu yi amfani da damar da doka ta ba mu ba, hakan zai zama tamkar mun aikata laifin ƙwarewa a matsayinmu na lauyoyi,” inji shi.

Afolabi ya kuma ƙaryata zargin cewa gwamnatin Amurka na hana fitar da bayanan ne da gangan domin kare Shugaba Tinubu. Ya yi nuni da wata sabuwar takardar da Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ta gabatar a gaban kotu, inda ya ce gwamnatin ta fi damuwa da yadda aka samo bayanan da kuma kare mutanen da suka shiga cikin binciken.

A cewarsa, a cikin bayanin da Ma’aikatar Shari’ar ta gabatar, an bayyana cewa damuwar gwamnati tana da alaƙa ne da hanyoyin da aka bi wajen tattara bayanan, ba wai kare Shugaba Tinubu ba.

“Ba a ambaci ko’ina cewa ana ba Shugaba Bola Ahmed Tinubu wata kariya ba,” inji shi.

Lauyan ya ce saboda tsananin da Amurka ke ɗauka kan laifin safarar miyagun kwayoyi, da wuya mutum ya kasance akwai isasshiyar hujja a kansa amma hukumomin ƙasar su bar shi yana shiga da fita ba tare da an kama shi ko an gurfanar da shi ba.

Ya tambayi dalilin da ya sa Tinubu ya ci gaba da yin tafiye-tafiye zuwa Amurka da dawowa tsawon shekaru ba tare da an kama shi ko an gurfanar da shi ba, idan har hukumomin Amurkan na da hujjar cewa yana da hannu wajen safarar hodar iblis heroin.

Afolabi ya kawo misalan tsohon shugaban Panama, Manuel Noriega, da tsohon Firaministan Tsibirin ɓirgin na Birtaniya, Andrew Fahie, da wasu mutane, domin nuna yadda hukumomin Amurka suka taɓa ɗaukar mataki kan manyan mutane da ake zargi da laifukan da suka shafi miyagun kwayoyi.

“Me ya sa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai kasance na musamman har ya riƙa shigowa Amurka ya fita ba tare da an kama shi, an tsare shi ko an yi masa tambayoyi kan wani abu ba?” ya tambaya. Ya kuma ƙara da cewa, kasancewar babu wata tuhuma ta aikata laifi da aka gabatar a kansa a gaban kotu na da muhimmanci, yana mai jaddada cewa mutum ba shi da laifi har sai an tabbatar da laifinsa.

By ukarofi

Leave a Reply