Dan Boko Haram ya miƙa wuya, sojoji sun daƙile zirga-zirgar ƙungiyar

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wani ƙasurgumin ɗan ƙungiyar Boko Haram ya miƙa wuya ga dakarun Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Gabas, wato Operation HADIN KAI, a garin Pulka da yake ƙaramar Hukumar Gwoza ta Jihar Borno, yayin da sojoji ke ci gaba da matsa wa ƙungiyoyin ’yan ta’adda lamba faɗin a yankin.

Dan ta’addar ya miƙa wuya ga sojojin da kansa da misalin ƙarfe 9:20 na safiyar Laraba, 2 ga Satumba, 2026, kamar yadda Muaaddashin Jami’in Yaɗa Labarai na Hedikwatar Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Gabas, Operation HADIN KAI, Kyaftin Mohammed Goni, ya bayyana a cikin wata sanarwa. Bayanan farko sun nuna cewa ɗan ta’addan ya taɓa gudanar da ayyukansa ne a yankin tsaunukan Mandara, da ke kan iyakar Nijeriya da Kamaru, wanda aka daɗe ana danganta shi da ayyukan ƙungiyoyin ’yan ta’adda.

A lokacin da ya miƙa wuyar, sojojin sun ƙwato daga hannunsa na’urar harba rokar RPG guda ɗaya, bom ɗin RPG guda ɗaya da kuma wayar hannu. Sanarwar ta ce, a halin yanzu ana gudanar da binciken farko da tantance bayanan ɗan ta’addan, bisa tsarin da rundunar soji ta tanada.

Kwamandan Rundunar Soji ta Fagen Aiki ya ce wannan ci gaba na nuna tasirin matsin lambar da dakarun ke ci gaba da yi kan hanyoyin sadarwa da ayyukan ƙungiyoyin ’yan ta’adda, da kuma raguwar damar da suke da ita ta gudanar da ayyukansu cikin ’yanci a yankin. Rundunar ta ƙara da cewa miƙa wuyar na ƙara nuna irin ƙoƙarin da Operation HADIN KAI ke yi wajen raunana ƙarfin ’yan ta’adda, tare da ƙarfafa sauran waɗanda ke ɗauke da makamai su ajiye su, su yi watsi da ta’addanci, su rungumi zaman lafiya.

Kwamandan Rundunar Soji ta Fagen Aiki ya sake tabbatar da ƙudurin rundunar na ci gaba da matsa wa ’yan ta’adda lamba, hana su damar gudanar da ayyukansu cikin ’yanci, da kuma samar da yanayin da zai taimaka wajen tabbatar da ɗorewar zaman lafiya da tsaro a yankin Arewa maso Gabas.

A wani rahoton kuma, dakarun Operation HADIN KAI sun daƙile yunƙurin ’yan ta’addan Boko Haram na yin zirga-zirga a Jihar Yobe, inda suka kashe ɗan ta’adda guda tare da ƙwato bindiga da alburusai a wani samame da suka gudanar bisa sahihan bayanan sirri.

An gudanar da aikin ne a ranar 1 ga Satumba, 2026, a ƙarƙashin jagorancin dakarun Bataliya ta 120 ta Rundunar Sojojin ƙasa, da ke ƙarƙashin Sashe na Biyu, tare da haɗin gwiwar ’yan ƙungiyar Fararen Hula Masu Taimaka Wa Sojoji (CJTF), a kan wata hanya da ake zargin ’yan ta’adda na amfani da ita a yankin Lamusuri, ƙaramar Hukumar Gujba ta jihar.

A cikin wata sanarwa da Muƙaddashin Jami’in Yaɗa Labarai na Hedikwatar Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Gabas, Operation HADIN KAI, Kyaftin Mohammed Goni, ya fitar, ya ce dakarun sun hango wasu ’yan ta’addan Boko Haram a kan hanyar ne bayan samun sahihin bayanan sirri.

Ya ce sojojin sun buɗe wuta kan ’yan ta’addan, lamarin da ya tilasta musu tserewa daga yankin. ɗan ta’adda guda ya mutu sakamakon musayar wutar, yayin da wasu daga cikin sauran suka tsere, bisa zargin cewa sun samu raunukan harbin bindiga.

A yayin samamen, dakarun sun kuma kwato bindigar AK-47 guda ɗaya, cajar bindiga guda uku, harsasai 90 na musamman masu girman 7.62mm da kuma jaka guda da ake ratayawa a jiki domin ɗaukar kayan yaƙi.

Kyaftin Goni ya ce nasarar aikin ta ƙara nuna ƙudurin dakarun Operation HADIN KAI na daƙile zirga-zirgar ’yan ta’adda da rage musu ƙarfin gudanar da hare-hare a yankin Arewa maso Gabas. Ya ƙara da cewa dakarun za su ci gaba da gudanar da samamen farmaki kan ’yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka a yankunan da ke ƙarƙashin ikon Rundunar Haɗin Gwiwa.

By ukarofi