
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Darakta-Janar na Hukumar Tsaro ta Farin kaya DSS, Oluwatosin Ajayi, ya umarci jami’an hukumar da kada su sake kama wani akan rikice-rikicen da suka shafi zamantakewar fararen hula.
Ajayi ya bayyana haka ne yayin wata hira da ‘yan jarida a ranar Alhamis a Abuja, ina ya bayyana cewa umarnin wani ɓangare ne na ɗaukar matakan ƙarfafa biyayya ga hukunce-hukuncen da dokar ƙasa ta tanada da kuma inganta tarihin hukumar kan kiyaye ‘yancin ɗan-adam.
Shugaban na DSS ya ce tunda ya kama aikin jagorantar hukumar, ya samar da gyare-gyare a sassa biyar da suka haɗa da tabbatar da biyayya ga doka, haɗin-gwiwa tsakanin hukumomi, tsare gaskiya da adalci, girmama ‘yancin ɗan-adam da gyare-gyare a harkokin walwala da gudanarwa da nufin inganta ayyukan hukumar.
A cewarsa, waɗannan gyare-gyare sun taimaka wajen bambance tsakanin rikicin zamantakewa da manyan laifuka acikin hukumar, yana mai cewa a baya hukumar tana gwama ɓangarorin biyu bisa kuskure. Ya bayyana cewa ba a amfani da ƙarfin iko wajen warware rikice-rikicen zamantakewa. “Ba za ka yi amfani da ƙarfi a rikice-rikicen zamantakewa ba. Ko da wasu manyan laifuka ma ba sa buƙatar ƙarfi”, inji shi.
Ya bayar da misali da Cibiyar tabbatar da tsare gaskiya da adalci a harkokin ƙasa (SERAP), inda ya ce ta garzaya kotu kan zarge-zargen jami’an DSS biyu da sun kai samame a farfajiyarta. Ya bayyana cewa a yayin haka ne aka je kotu, inda daga ƙarshe kotun ta nemi da biya SERAP diyyar Naira miliyan 100 kan zargin ɓata suna a watan Mayu, 2026.
Akan haka ne ya shawarci jami’an nasu da su riƙa tura masu rikice-rikicen zamantakewa zuwa kotuna domin warware su da kuma biyayya ga dokar ƙasa don kare mutuncin ayyuka da ƙwarewarsu.
