Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kwamitin wucin gadi na Majalisar Wakilai da ke binciken ayyukan wata ƙungiya da ake kira Presidential Foreign Inɓestment Promotion Council (PFIPC) ya bayyana cewa ba a kafa ƙungiyar bisa ƙa’ida ba, tare da bayyana ta a matsayin hukumar gwamnati ta bogi.
A cikin sakamakon bincikensa na farko da aka fitar ranar Laraba, kwamitin ya kuma ce takardar naɗin Adeyemi Adeniyi a matsayin Darakta-Janar na PFIPC ba ta da inganci, yayin da ya gano asusun banki 58 da ma’aikata 39 da ake alaƙanta su da wanda ake zargin.
Binciken ya kuma wanke tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, daga hannu a ayyukan wannan ƙungiya da ake zargi da zama ta bogi.
Shugaban kwamitin, Hon. Ibrahim Sani Madaki, ya yaba wa Gbajabiamila bisa sanar da hukumomi game da samuwar da ayyukan ƙungiyar, yana mai cewa matakin nasa ya taimaka wajen tona wata ƙungiyar hukumomi da ake zargin suna fakewa da sunan hukumomin gwamnati.
A yayin zaman kwamitin ranar Laraba, ’yan majalisar sun ce bayanan farko da suka samu sun nuna cewa sama da asusu 30 daga cikin asusun banki 58 da aka gano ana gudanar da su ne da sunayen hukumomi, kamfanoni, gidauniyoyi da wasu ƙungiyoyi masu alaƙa da juna.
Kwamitin, ƙarƙashin jagorancin Yusuf Gagdi, ya ce an haɗa waɗannan asusun ta hanyar bayanan Bank ɓerification Number (BVN) da sauran bayanan tantance mutum da ke alaƙanta su da Prince Adeniyi Adeyemi, wanda ake gabatarwa a matsayin Darakta-Janar na ƙungiyar.
Sai dai kwamitin ya bayyana cewa har yanzu bai yanke hukunci cewa dukkan asusun, ƙungiyoyi ko mu’amalolin da aka gano haramtattu ba ne, domin bincike kan rajistar ƙungiyoyin, masu mallaka, masu sa hannu da tarihin mu’amalolin kuɗi na ci gaba.
Binciken ya biyo bayan wani ƙuduri da Majalisar Wakilai ta amince da shi ranar 8 ga Yuli, 2026, wanda ya bai wa kwamitin damar binciken yadda aka shigar da PFIPC cikin tsarin kasafin kuɗin Tarayya.
Kwamitin ya ce bincikensa ya nuna cewa babu wata doka ko ingantaccen takardar gwamnati da ta kafa PFIPC, duk da yadda ƙungiyar ke gabatar da kanta a matsayin wata hukuma ta gwamnatin Tarayya.
Haka kuma, binciken ya gano cewa akwai kusan mutane 39 da aka gabatar ko aka ɗauka a matsayin ma’aikatan ƙungiyar a matakai daban-daban.
Kwamitin ya ce yana binciken yadda aka ɗauki waɗannan ma’aikata, takardun aikinsu, katunan shaida, albashi da alawus-alawus da aka ce ana ba su, da kuma zargin cewa an buƙaci wasu mutane su biya kuɗi domin samun aiki.
Majalisar ta ce za ta bambanta tsakanin waɗanda wataƙila aka yaudare su suka yi imanin cewa ƙungiyar ta gaskiya ce, da waɗanda suka san cewa ba ta da inganci amma suka shiga ko suka amfana da ayyukanta.
Baya ga PFIPC, kwamitin ya ce ya gano wasu ƙungiyoyi 12 da ake zargin suna gudanar da ayyuka ba bisa ƙa’ida ba, tare da gabatar da kansu kamar hukumomin gwamnati.
A cewar kwamitin, akwai fiye da ƙungiyoyi 12 da ake alaƙanta su kai tsaye ko a kaikaice da Adeyemi.
Daga cikin sunayen da aka bayyana akwai FCT Inɓestment Promotion Council, FCT Inɓestment Promotion Agency and Public-Priɓate Partnership, United Nations Youth Global Foundation da Olubadan of Ibadan Foundation.
Sauran sun haɗa da Confederation of United Nations Youths, Foreign Inɓestment Promotion Agency, United Nations Youth Global Agency, World United Nations Youth Global Foundation, World Entrepreneurship Uniɓersity Limited, World Enterprise Uniɓersity Limited, FCT Inɓestment Promotion Act da FCT Promotion Agency.
Kwamitin ya ce kamanceceniya tsakanin sunayen ƙungiyoyin, manufofinsu, tsarin shugabanci, masu sa hannu da alaƙar asusun bankinsu ya haifar da zargin cewa an kafa ko aka yi amfani da wasu ƙungiyoyin ne domin samun amincewa ta hanyar amfani da sunayen gwamnati, ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, zuba jari, ilimi, ayyukan agaji ko Majalisar ɗinkin Duniya.
Masu binciken na kuma ƙoƙarin gano ko an yi amfani da waɗannan ƙungiyoyi wajen gina amincewa ta bogi, neman kuɗi ko jari, samun wasu damar gwamnati ko kuma yaudarar jama’a domin su bayar da kuɗinsu.
Kwamitin ya kuma ce wani kamfani ya yi zargin cewa Adeyemi ya sa ya biya kusan Naira miliyan 400 a kashi huɗu, bayan an yi masa alƙawarin samun kwangilar gyara, samar da kayan daki ko inganta wani gida da aka ce an ware wa Adeyemi a matsayin gidan Darakta-Janar.
A cewar kwamitin, wakilan kamfanin sun ce an kai su wani gida a Abuja, inda aka gaya musu cewa shi ne gidan aikin wanda ake gabatarwa a matsayin Darakta-Janar.
Yanzu haka ana bin diddigin kuɗaɗen, masu mallakar asusun da kuma masu cin gajiyar kuɗaɗen, tare da binciken mallaka da matsayin gidan da ake magana a kai.
Kwamitin ya ce idan binciken hukumomi da shari’a ya tabbatar da waɗannan zarge-zarge, za su iya zama laifuffukan bayar da bayanan ƙarya domin yaudara, karɓar kuɗi ta hanyar yaudara, kwaikwayon hukuma ko mutum, haɗa baki da kuma ƙirƙirar takardun bogi.
Binciken ya kuma nuna cewa babu wata ingantacciyar dokar Majalisar Tarayya, umarnin shugaban ƙasa, sanarwar gwamnati ko wata takarda mai inganci da ta kafa PFIPC.
Kwamitin ya ce babu wata hukumar gwamnatin Tarayya da ta gabatar da sahihiyar takarda da ke tabbatar da cewa an kafa ko amince da ƙungiyar a hukumance.
Haka kuma, an ce takardun da aka yi amfani da su wajen gabatar da PFIPC a matsayin hukumar gwamnati sun ƙunshi alamun ƙirƙira, jabu, canza bayanai da kuma kwaikwayon wasu hukumomi.
ɗaya daga cikin takardun da aka bincika ita ce wata wasiƙar naɗin Adeyemi a matsayin Darakta-Janar, wadda aka ce ta fito daga Shugaban ƙasa kuma tana ɗauke da sa hannun tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila.
Sai dai Fadar Shugaban ƙasa, a cewar kwamitin, ta tabbatar da cewa ba a taɓa yin irin wannan naɗi ko amincewa da shi ba, kuma Gbajabiamila bai rubuta ko sanya hannu kan wasiƙar ba.
Kwamitin ya kuma ce takardar da aka yi amfani da ita ba ta yi daidai da sahihin tsarin takardun Fadar Shugaban ƙasa ba, yayin da lambar wasiƙar, tsarinta, harshen da aka yi amfani da shi da sauran bayananta suka saɓa da tsarin wasiƙun gwamnati.
Haka kuma, kwamitin ya binciki wata takarda da aka gabatar a matsayin Presidential Eɗecutiɓe Order No. 5 mai kwanan watan 24 ga Fabrairu, 2026, amma ya ce binciken ya nuna cewa ba sahihin umarnin shugaban ƙasa ba ne kuma ba a fitar da shi ta hanyar da doka ta tanada.
Wata takarda kuma da aka gabatar a matsayin dokar Majalisar Tarayya da ta kafa ƙungiyar, kwamitin ya ce ba Majalisar Dokoki ta kafa ta ba, ba majalisun biyu suka amince da ita ba, shugaban ƙasa bai sanya mata hannu ba kuma ba a wallafa ta a hukumance ba.
An kuma gano wasu sassan wata takarda da suka shafi wata hukuma daban da ake zargin an yi musu sauye-sauye ta hanyar fasahar kwamfuta domin a nuna kamar Majalisar Tarayya ta kafa PFIPC.
Binciken ya kuma gano wata wasiƙa mai kwanan watan 7 ga Nuwamba, 2024, wadda ake zargin an tura ta daga Fadar Shugaban ƙasa zuwa Ofishin Akanta-Janar na Tarayya domin neman lambar gudanarwa ga PFIPC.
Wasiƙar ta ɗauke da sunan wani mutum mai suna Akambi Adewale, wanda aka bayyana a matsayin darekta a wata hukumar Fadar Shugaban ƙasa.
Sai dai Fadar Shugaban ƙasa ta shaida wa kwamitin cewa babu irin wannan ofishi ko darakta kamar yadda aka bayyana, kuma babu wani jami’i mai suna Akambi Adewale da ya taɓa riƙe wannan muƙami.
Kwamitin ya ce wannan bincike ya haifar da manyan tambayoyi kan ayyukan wasu mutane da ƙungiyoyi da ake zargi da gabatar da kansu a matsayin sahihan hukumomin gwamnati tare da gudanar da ayyuka ba tare da izini ba.
Majalisar Wakilai ta ce binciken yana ci gaba, kuma za ta gabatar da ƙarin shawarwari bayan kammala bincike kan PFIPC da sauran ƙungiyoyin da aka gano.
