Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano
Mai magana da yawun ƙungiyar Tsofaffin Daliban Tsohon Kwalejin Horar da Malamai da ke Wudil, Ambasada M. K. Adam Rano, ya bayyana cewa tarukan ƙungiyoyin tsofaffin dalibai na makarantu ana shirya su ne domin sada zumunci da ƙarfafa alaƙa tsakanin abokan karatu.
Rano ya bayyana hakan ne yayin bikin cikar shekaru 35 da kafa ƙungiyar, wanda aka gudanar a ɗakin motsa jiki na tsohuwar kwalejin da ke Wudil a makon da ya gabata.
Ya ce babban makasudin shirya taron shi ne bikin cikar ƙungiyar shekaru 35 da kuma bai wa tsofaffin daliban damar sake haɗuwa da juna bayan kammala karatunsu.
A cewarsa, irin wannan taro yana taimakawa wajen tunawa da waɗanda suka rasu bayan kammala karatu, tare da sanin halin da abokan karatu suke ciki bayan rabuwa da makaranta.
“Muna haɗuwa ne domin mu riƙa sada zumunci, mu tallafa wa junanmu, mu yi wa waɗanda suka rasu addu’a, sannan mu yi wa juna fatan alheri. Wannan shi ne babban makasudin shirya wannan taro.
“Kamar yadda kuka gani, mun gayyato har waɗanda suka kammala karatu tun a shekarar 1972, tare da tsofaffin malamanmu da muka karrama saboda irin gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban rayuwarmu,” in ji shi.
Wasu daga cikin mahalarta taron sun bayyana farin cikinsu tare da gode wa Allah da Ya ba su damar halartar bikin cikar ƙungiyar shekaru 35 bayan kammala karatunsu.
Sun ce manufar taron ita ce ƙara jaddada alaƙa da tunawa da juna, domin ƙarfafa zumuncin da ya haɗa su tun lokacin da suke dalibai a kwalejin.
Mahartan taron sun kuma bayyana cewa suna shirya irin wannan taro a kowace shekara, inda suke tallafa wa iyalan waɗanda suka rasu bayan kammala karatu, domin nuna irin kyakkyawar alaƙar da suka kasance da ita tun lokacin da suke raye.
A yayin taron, an karrama wasu daga cikin tsofaffin malaman da suke raye, tare da wasu daga cikin mambobin ƙungiyar da suka bayar da gagarumar gudunmawa wajen ci gaban ƙungiyar. Haka kuma, an bayar da tallafi ga iyalan wasu daga cikin mambobin da suka rasu.
Taron ya samu halartar tsofaffin daliban da suka kammala karatu tun daga shekarar 1972 har zuwa lokacin da aka mayar da kwalejin zuwa Jami’ar Kimiyya da Fasaha mallakin Jihar Kano, tare da wasu daga cikin tsofaffin malaman makarantar.
