Daga RABIU SANUSI a Kano
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi kakkausar suka kan hare-haren ’yan bindiga da aka kai a wasu sassan ƙananan hukumomi huɗu na jihar, inda ya tabbatar wa al’ummomin da lamarin ya shafa cewa gwamnatinsa na ɗaukar matakan da suka dace domin ƙara ƙarfafa tsaro da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Talata.
Yankunan da hare-haren suka shafa sun haɗa da Chiromawa da ke ƙaramar Hukumar Garun Malam, Beli da ke ƙaramar Hukumar Rogo, Bebeji, da kuma wasu al’ummomin da ke kewaye da ƙaramar Hukumar Gwarzo.
Gwamna Yusuf ya miƙa saƙon ta’aziyya da jaje ga waɗanda lamarin ya rutsa da su da kuma iyalan waɗanda abin ya shafa, inda ya bayyana hare-haren a matsayin abin matuƙar tayar da hankali wanda ba za a amince da shi ba.
Gwamnan ya tabbatar wa al’ummomin da abin ya shafa cewa gwamnati za ta ɗauki dukkan matakan da suka dace, tare da haɗin gwiwa da hukumomin tsaro, domin dakile sake aukuwar irin waɗannan hare-hare da kuma dawo da kwarin gwiwar jama’a kan harkokin tsaro.
Ya ce an umarci hukumomin da abin ya shafa da su ƙara ƙarfafa sa ido, tattara bayanan sirri da kuma inganta tsarin ɗaukar matakin gaggawa a yankunan da hare-haren suka faru.
Gwamna Yusuf ya yi kira ga mazauna yankunan da abin ya shafa da su kwantar da hankulansu tare da kauce wa duk wani mataki da ka iya ƙara dagula al’amura ko haifar da tashin hankali.
Ya tabbatar musu cewa gwamnatin jihar na aiki kafaɗa da kafaɗa da jami’an tsaro domin shawo kan matsalar tare da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a.
Haka kuma, gwamnan ya buƙaci al’umma da su bai wa jami’an tsaro cikakken haɗin kai tare da samar musu da sahihan bayanan sirri da za su taimaka wajen dakile hare-haren, gano tare da cafke waɗanda ke da hannu wajen aikata laifukan.
Ya yaba wa jami’an tsaro bisa ƙoƙarin da suke yi, tare da buƙatarsu da su ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro bisa sahihan bayanan sirri domin kare al’ummomin da ke cikin haɗari a faɗin jihar.
Gwamna Yusuf ya yi addu’ar Allah Ya jiƙan waɗanda suka rasa rayukansu, Ya ba waɗanda suka jikkata lafiya cikin gaggawa, sannan Ya dawo da duk wani mutum da aka yi garkuwa da shi cikin aminci.
Ya sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Jihar Kano baki ɗaya, tare da tabbatar da zaman lafiya da tsaro mai dorewa a dukkan sassan jihar.
