Wike ya zargi gwamnonin Imo da Kwara da yi masa zagon ƙasa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma, da Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaƙ, a matsayin gwamnonin APC biyu da yake zargin suna aiki da tsare-tsaren siyasa da suka saɓa wa muradunsa gabanin zaɓen 2027.

Wike ya yi wannan zargi ne yayin wata tattaunawa da manema labarai a Port Harcourt, babban birnin Jihar Riɓers, inda ya kuma yi watsi da zargin cewa ayyukansa na siyasa na da nufin yi wa gwamnonin APC zagon ƙasa.

Tsohon Gwamnan Jihar Ribas ya fi karkata suka kan Gwamna AbdulRazaƙ, inda ya zarge shi da jagorantar wani gangamin siyasa da ake yi masa.

A cewar Wike, ya taɓa tunkarar Gwamnan Kwara kai tsaye kan lamarin, yana mai cewa ba ya faɗin abin da ba zai iya karewa ba.

Wike ya ce AbdulRazaƙ ya zarge shi da tallafa wa wasu ’yan siyasa da ba sa goyon bayan ’yan takarar da gwamnan ya fi so a Jihar Kwara.

Sai dai Wike ya ce maimakon hakan, Gwamnan Kwara ya kamata ya yaba masa saboda rawar da ya taka wajen bai wa wasu ’yan siyasar APC da suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar PDP damar ci gaba da harkokinsu na siyasa.

Game da Gwamna Hope Uzodinma na Jihar Imo, Wike ya ce gwamnan ya san irin goyon bayan siyasa da ya taɓa ba shi, amma ya nuna cewa dangantakarsu ta samu tangarɗa a wasu lokuta.

Duk da sabanin da ke tsakaninsa da gwamnonin biyu, Wike ya jaddada cewa hakan ba zai karkatar da hankalinsa daga manufarsa ta tabbatar da sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027 ba.

Wike, wanda har yanzu yake cikin jam’iyyar PDP amma yake bayyana goyon bayansa ga tazarcen Tinubu, ya ce ba ya ɓoye matsayinsa na siyasa kuma ba zai ja da baya daga ƙoƙarinsa na ganin shugaban ƙasa ya sake lashe zaɓe ba.

By ukarofi