Makarantar St. Louis ta yi walimar saukar Alƙur’ani karo na 21 a Kano

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Makarantar ’yan mata ta St. Louis da ke Kano ta shirya walimar saukar Alƙur’ani Mai Girma karo na 21, inda ɗalibai 47 suka kammala karatun Alƙur’ani.

Makarantar, wadda ta cika shekaru 75 da kafuwa, ta gudanar da taron ne domin taya ɗaliban murnar wannan gagarumar nasara.

Mataimakiyar shugaban makarantar, Malama Halima Baba Yaro, ta bayyana a wajen taron cewa makarantar tana da tsari na musamman wajen koyar da Alƙur’ani Mai Girma da kuma ilimin addini.

Ta ce manufar wannan tsari ita ce bai wa ɗalibai damar fahimtar addini tare da samun kyakkyawar tarbiyya da sanin ya kamata.

Malama Halima Baba Yaro ta ce makarantar ta tsaya tsayin daka wajen tabbatar da samar da ɗalibai masu tarbiyya, tsoron Allah da kuma kyawawan halaye.

Ta ce babban burin malaman makarantar shi ne ganin sun samar da ɗalibai nagari waɗanda iyayensu da al’umma za su yi alfahari da su.

A cewarta, kamar yadda iyaye ke son ganin sun haifi ’ya’ya tare da renonsu cikin kyakkyawar tarbiyya, haka makarantar St. Louis ke ƙoƙarin cika nata nauyin wajen gina ɗalibai masu ilimi da ɗabi’a nagari.

Ta kuma jaddada buƙatar iyaye su ci gaba da sanya ido kan tarbiyyar ’ya’yansu, musamman bayan sun kammala karatunsu a makaranta.

A nasa jawabin, ɗaya daga cikin iyayen da suka halarci taron, Dakta Alhaji Salisu Ibrahim Zubairu, ya taya ɗaliban murnar kammala saukar Alƙur’ani.

Ya buƙace su da su fahimci cewa wannan nasara ita ce matakin farko na neman ilimin addini da na zamani, yana mai kira gare su da su ci gaba da nazari da maimaita abin da suka koya.

Ya ce ilimi ba zai amfani mutum da al’umma ba sai an yi aiki da shi tare da ci gaba da neman ƙarin ilimi.

Wasu daga cikin ɗaliban da suka halarci taron sun haɗa da Fatima Ibrahim, Zubaidu Ali da Fatima Sani, waɗanda suka yi addu’o’in fatan alheri ga malamansu, iyayensu da kuma sauran al’umma.

Walima ta gudana cikin farin ciki da addu’o’i, yayin da iyaye, malamai da sauran mahalarta suka taya ɗaliban murnar wannan gagarumar nasara.

By ukarofi