2027: Mun yi shiri tsaf domin nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf — APC Ungogo

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Wani jigo a Jam’iyyar APC kuma shugaban Karta Kwana na Ilimi a ƙaramar Hukumar Ungogo, Alhaji Sammani Muhammad Abdulmumin Zango, ya ce sun yi shiri tsaf domin tabbatar da nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf a zaɓen gwamnan Jihar Kano na shekarar 2027, da yardar Allah.

Alhaji Zango ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano.

Ya ce zuwa yanzu alamu sun nuna cewa al’ummar Jihar Kano, maza da mata, musamman masu kaɗa ƙuri’a, suna tare da Gwamna Abba Kabir Yusuf kuma za su sake zaɓensa a shekarar 2027.

“Dalilin hakan shi ne, al’umma sun gamsu da yadda yake ci gaba da gudanar da ayyukan ci gaba da kuma ƙoƙarin kawo sauƙi ga rayuwar jama’a,” inji shi.

Alhaji Zango ya ce rabuwar Gwamna Abba Kabir Yusuf da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ba za ta hana gwamnan samun nasara a zaɓen 2027 ba.

A cewarsa, jama’a ne ke zaɓen shugabanni, ba mutum ɗaya ba.

Ya ce APC a ƙaramar Hukumar Ungogo da ma faɗin Jihar Kano suna ci gaba da shirye-shiryen ƙarfafa jam’iyyar a matakin ƙasa domin tabbatar da gagarumar nasara ga Gwamna Abba Kabir Yusuf.

A ɓangaren zaɓen shugaban ƙasa, Alhaji Sammani Zango ya yi kira ga al’ummar Jihar Kano da su sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2027.

Ya ce Shugaba Tinubu na ƙoƙari wajen haɗa kan al’umma da kuma ’ya’yan Jam’iyyar APC, tare da ƙoƙarin sasanta duk wata baraka da ta taso a cikin jam’iyyar.

Zango ya ce haɗin kai tsakanin shugabannin jam’iyyar da magoya bayanta zai taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da nasarar APC a dukkan matakai a zaɓen 2027.

A ƙarshe, Alhaji Sammani Zango ya yi kira ga shugabannin Arewa, musamman masu riƙe da madafun iko, da su ci gaba da taimaka wa al’ummominsu domin samun ci gaba, zaman lafiya da walwalar jama’a.

Ya kuma buƙaci ’yan siyasa da su sanya maslahar jama’a da ci gaban ƙasa a gaba, tare da kauce wa duk wani abu da zai iya kawo rabuwar kai ko rashin zaman lafiya.

By ukarofi

Leave a Reply