Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano
Shugaban ƙaramar Hukumar Warawa, Alhaji Lamido Sunusi Ahmad, ya karɓi sama da mutum 500 da suka sauya sheƙa daga jam’iyyun PDP da NDC zuwa Jam’iyyar APC.
An karɓi sabbin mambobin jam’iyyar ne daga mazabar Garin Dau, a wani taro da aka gudanar a gidan shugaban ƙaramar hukumar da ke Garin Dau a ranar Talata.
Da yake karɓar masu sauya sheƙar, Alhaji Lamido Sunusi Ahmad ya bayyana ranar a matsayin mai matuƙar muhimmanci a gare shi.
Ya ce kusan kullum ana samun mutanen da ke barin wasu jam’iyyu domin shiga APC, sakamakon yadda Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ke gudanar da mulkinsu.
Shugaban ƙaramar Hukumar ya bai wa sabbin mambobin tabbacin cewa za a ba su damar shiga cikin harkokin jam’iyyar tare da amfana da duk wani tsari da ya shafi siyasa.
Ya kuma yi kira gare su da su tsaya tsayin daka wajen yi wa APC aiki domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a zaɓe mai zuwa.
“A halin yanzu babu wata jam’iyya da ake magana a kanta kamar APC, musamman idan aka yi la’akari da irin ayyukan ci gaba da take kawowa al’umma a fannoni daban-daban,” in ji shi.
Lamiɗo Sunusi Ahmad ya kuma yaba wa shugabannin addini bisa irin rawar da suke takawa wajen fadakar da al’umma kan muhimmancin zaɓen shugabanni nagari masu kawo ayyukan raya ƙasa da ci gaba.
Shi ma a jawabinsa, ɗaya daga cikin jagororin APC a mazabar Garin Dau, Alhaji Nura Shehu Garin Dau, wanda kuma jami’i ne mai kula da hulɗa da jin daɗin alhazai a ƙaramar Hukumar Warawa, ya bayyana farin cikinsa kan yadda al’umma ke ci gaba da shiga APC.
Ya ce abin da ke ƙara jawo hankalin jama’a zuwa jam’iyyar shi ne irin yadda Gwamnan Jihar Kano ke gudanar da harkokin al’umma.
Ya kuma bayyana shugaban ƙaramar Hukumar Warawa a matsayin jajirtaccen shugaba da ya kawo ayyukan ci gaba cikin ɗan gajeren lokacin da ya shafe yana jagorantar ƙaramar hukumar.
A madadin sauran masu sauya sheƙar, Dahiru Adamu na PDP da Abdullahi Isyaku na NDC sun ce dalilin da ya sa suka bar jam’iyyunsu zuwa APC shi ne irin ayyukan ci gaban da shugaban ƙaramar hukumar ke gudanarwa a yankin.
Sun ce daga cikin ayyukan da suka ba su ƙwarin gwiwar shiga APC akwai gyaran magudanan ruwa, makarantu da asibitoci, samar da tallafin jari ga matasa maza da mata, da kuma gyaran hanyoyi domin bunƙasa harkar sufuri.
Taron ya samu halartar shugabannin jam’iyyar APC na mazabar Garin Dau, wakilan kansiloli da kuma masu bai wa shugaban ƙaramar hukumar shawara.
