Hukumomin shari’a a Faransa sun sanya wani matashi mai shekaru 18 a ƙarƙashin bincike na hukuma, bisa zargin hannu a jerin hare-haren kutsawa gidaje da ƙarfi da kuma shirye-shiryen sace attajirai, ciki har da ɗan wasan Real Madrid da tawagar Faransa, Kylian Mbappe.
Jaridar Le Parisien ta Faransa ta ruwaito cewa an gurfanar da matashin, wanda aka bayyana sunansa da Clement L., tare da wani da ake zargi abokin aikinsa, a ranar 21 ga Agusta a Nanterre, da ke Hauts-de-Seine, kan zargin aikata laifukan fashi cikin tsari na ƙungiya.
Rahotanni sun ce masu bincike na zargin matashin da kasancewa wanda ke jagorantar ƙungiyar da ta shirya ko kuma ta aikata jerin hare-hare da yunƙurin sace mutane tsakanin 11 ga Afrilu zuwa 19 ga Agusta a wasu sassan Faransa.
A cewar rahoton, Mbappe na cikin mutane 26 da ake zargin ƙungiyar ta sanya a jerin waɗanda za ta iya kai wa hari.
Daga cikin waɗanda ake zargin an yi wa niyya akwai ’yan kasuwa masu hannu da shuni, wani mawaƙin rap da kuma ɗan wasan Real Madrid ɗin, inda ake zargin ƙungiyar ta shirya sace wasu daga cikinsu tare da yi musu mugun duka.
Wannan zargi ya sake jawo hankalin jama’a kan matsalar tsaron da fitattun ’yan ƙwallon ƙafa ke fuskanta a Faransa da sauran ƙasashen Turai, musamman saboda dukiyarsu da shahararsu da ke sanya su zama abin sha’awa ga ƙungiyoyin masu aikata manyan laifuka.
Sai dai babu wani bayani da ya nuna cewa an kai wa Mbappe hari a zahiri ko kuma an riga an yi wani yunƙurin sace shi.
