
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Alhamis wasu da ake zargin ‘yan Boko Haram ne, sun kai hari ga wa tawagar motocin ɗan takarar gwamna a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar APC a Jihar Borno, Injiniya Mustapha Gubio, inda aka samu fashewar boma-bomai da harbe-harbe a yankin babban titin Gubio zuwa Kareto zuwa Damasak.
A cewar majiyoyi, al’amarin ya auku ne yayin da Mustapha Gubio da ‘yan tawagarsa suke koma wa Maiduguri bayan ziyarar godiya a yankin iyaka da garin Damasak. Rahotanni sun bayyana cewa tawagar ta gamu da tsaiko ne a lokacin da aka yi zargin ‘yan ta’addar sun dasa ababen fashewa a yankin babban titin.
Wata majiyar tsaro da ta nemi a sakaye sunanta, ta ce mayaƙan sun dasa wasu boma-boman ne kan hanyar Gubio zuwa Kareto zuwa Damasak, inda motar yaƙi ta ‘yan sanda da ke jagorantar tawagar ta haye kan ɗaya daga cikinsu, lamarin da ya haddasa tarwatsewar sa.
Damasak wani yankin ne mai nisan kilomita 190 daga Maiduguri, babban birnin jihar, kuma tawagar ta je yankin ne da nufin cigaba da gudana da harkokin yaƙin zaɓen Gubio da jam’iyya APC.
Bayan fashewar boma-boman, mayaƙan sun yi yunƙurin yi wa tawagar kwanton-bauna, inda suka buɗe wuta ga motocin jami’an tsaro da sauran mambobin tafiyar.
Saidai, jami’an tsaro da suka haɗa da sojoji, ‘yan sanda da mambobin CJTF sun mayar da martani wajen yin musayar wuta da mayaƙan, lamarin da ya ba jami’an tsaro nasarar daƙile farmakin.
