An yi kira ga Gwamnan Katsina ya ɗauki matakin gaggawa kan yanayin tsaro a Funtua

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban ƙungiyar cigaban Funtua Kwamred Mannir Suleiman ya yi kira ga Gwamna Dikko Raɗɗa da ya ɗauki mataki na gaggawa domin kawo ƙarshen hare haren ‘yan bindiga a yankin Funtua musamman a cikin garin Funtua.

Kwamred Suleiman ya yi wannan kira a hira da manema labarai a Katsina, ya nuna damuwa a cikin mako biyu irin mummunar hare haren da ‘yan bindiga ke kai wa da ya yi sanadiyar rasa rayuka, jikkata jama’a da satar dabbobi.

“Sun kai hare hare a Kasuwar Mata, Unguwar Dahiru, Kasuwar Madalla Sokoto Bypass da Jabiri in da nan ma aka rasa rayuka da dama wasu suka sami raunuka a waɗannan wurare,”Inji Suleiman.

Ya bayyana cewar duk da jami’an tsaro na bakin ƙoƙarin su,ya kamata gwamna Dikko Raɗɗa ya ƙara ɗaukar matakai na dawo da zaman lafiya a yankin.

Shugaban ƙungiyar ya yi kira ga zaɓaɓbun wakilai a matakin ƙasa da jiha da masu riƙe da muƙaman siyasa da su haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen bada ta su gudummuwa wajen dawo da zaman lafiya.

Ya kuma kira ga limamai da su cigaba da gudanar da addu’o’i na ɗorewar zaman lafiya a yankin Funtua da Jihar Katsina baki ɗaya.

By ukarofi

Leave a Reply