Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar Kwastom ta Nijeriya ta ce ta kama bindigogi kirar pump-action 204 da aka ɓoye a cikin wani kwantena da ya isa tashar jirgin ruwa ta TinCan Island da ke Legas daga ƙasar Turkiyya.
An ɓoye makaman ne a tsakanin kayayyakin gida kamar kujeru, firinjoci, na’urorin hasken rana da kuma garin sabulu.
Jami’an kwastam sun ce sun gano su ne bayan bayanan sirri da suka samu suka sa aka yi cikakken bincike kan kwantenan.
Hukumar ta bayyana cewa bindigogin nau’in MAS 49 Alter Magnum pump-action rifles ne, kuma an gano wasu kayayyakin bindiga tare da su.
Wannan ne karo na biyu cikin makwanni ƙalilan da aka kama irin waɗannan makamai a tashar, bayan da aka gano wasu bindigogi 399 a wani kwantena a watan Agusta.
Jami’ai sun ce ana ci gaba da bincike domin gano waɗanda suka shigo da makaman da kuma waɗanda aka nufa a kai musu.
