Atiku ya koka kan yadda talauci ke sa matasa ke siyar da ƙodarsu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, ya bayyana damuwarsa kan abin da ya kira da yawaitar yadda matasan Nijeriya ke siyar da ƙodarsu saboda tsananin talauci da matsin rayuwa, yana mai ɗora laifin hakan kan tsare-tsaren tattali da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta samar.

Atiku, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na 2027 a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar ADC, ya bayyana haka ne a wani saƙo ta kafar X a ranar Alhamis, inda ya ce ya samu labarai masu tayar da hankali kan halin da matasa suka samu kansu a ciki na sayar da sassan jikkunansu musamman ƙoda domin su samu kuɗi.

Ya bayyana cewa, a madadin matasan Nijeriya suka riƙa siyar da basira da fasahar ƙirƙira da suka da ita, sun koma siyar da gaɓoɓin jiki, yana mai cewa hakan abu ne ya dace kowane ɗan ƙasa mai kishi ya nuna damuwa a kai.

Ya yi iƙirarin cewa, ana kwaɗaitar da matasan Nijeriya su siyar da ƙodarsu akan Naira miliyan 1.7 kacal, saidai bai danganta adadin kuɗin da wani rahoto ko hukuma ba.

Atiku dai ya alaƙanta wannan zargi ga halin matsin rayuwa da al’umma ke fuskanta a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu, inda ya zayyano abinci, sufuri, haya, makaranta, magani da lantarki a matsayin ababen da ke ƙoƙarin fin ƙarfin talakan Nijeriya a ƙarƙashin wannan gwamnatin.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa Nijeriya tana da dokokin da suke haramta cinikayyar sassan jiki ko safarar su, saidai ya ce dokokin ba za su iya magance talauci da kwaɗayin aikata miyagun laifuka ba a tsakanin matasa, yana mai kira ga a samar da gyare-gyaren tattali da za su taimaka wajen samun sauƙin siyan abinci, sufuri, kiwon lafiya, ayyuka masu daraja da sabunta fata ga masu tasowa.

By Babaji