Daga GAMBO ISA a Abuja
Kungiyar ZASCOSA ta ƙasa ta ƙaddamar da ƙananan kwamitoci guda 10 domin jagorantar ayyukan ƙungiyar da kuma sauƙaƙa shirye-shiryen taronta na shekara-shekara (AGM) da kuma Bikin Dinner da Raba Kyaututtuka da aka shirya gudanarwa a watan Nuwamban shekarar 2026.
Shugaban ZASCOSA na ƙasa, Esɓ. Dung Nehemiah Rwang, ne ya ƙaddamar da kwamitocin a ranar Asabar.
Rwang ya ce an zaɓi waɗanda za su jagoranci kwamitocin cikin tsanaki, bayan tuntuɓar shugabannin rassan ƙungiyar daban-daban ko wakilansu, bisa la’akari da ƙwarewa da gogewar da suke da ita a fannoni daban-daban.
Ya ce kafa kwamitocin ya zama wajibi domin shirye-shiryen manyan tarukan da ƙungiyar ke shirin gudanarwa, tare da kira ga mambobin kwamitocin da su nuna jajircewa da ƙwarewa wajen sauke nauyin da aka ɗora musu.
Da yake mayar da martani, Shugaban Kwamitin Ayyuka da Ci Gaba, Luther Shambor, ya gode wa shugabancin ƙungiyar bisa amincewar da aka yi da mambobin kwamitin, tare da tabbatar da aniyarsu ta haɗa kai wajen sauke nauyin da aka ɗora musu.
Sauran mambobin kwamitocin da suka haɗa da Abdul Lateef Lawal, Danladi Bature Danbwarang, Lami Pam da Funmilayo Anjorin, sun kuma nuna godiyarsu bisa damar da aka ba su, tare da alƙawarin bayar da gudummawarsu wajen bunƙasa tsohuwar makarantar da suka kammala.
Kananan kwamitocin guda 10 sun haɗa da Kwamitin Jin Daɗi da Kiwon Lafiya; Kuɗi da Tara Kuɗaɗe; Ayyuka da Ci Gaba; Membobi, Bayanan Mambobi da Rubuce-rubuce; Walwala, Nishaɗi da Haɗuwar Tsoffin Dalibai; Yaɗa Labarai da Harkokin Sadarwa; Shari’a da Bitar Kundin Tsarin Mulki; Ilimi da Jagoranci; Kasuwanci da Zuba Jari; da kuma Kwamitin ƙasashen Waje.
An bai wa Kwamitin Jin Daɗi da Kiwon Lafiya alhakin tallafa wa mambobin da ke fuskantar matsalolin rashin lafiya mai tsanani, rasuwar ’yan uwa da sauran matsalolin jin daɗi.
Haka kuma, kwamitin zai shirya tattaunawa kan harkokin lafiya, gudanar da ayyukan ba da kulawar lafiya ga al’umma da kuma shirye-shiryen inshorar lafiya.
Kwamitin Kuɗi da Tara Kuɗaɗe kuma zai kula da kuɗaɗen membobinsu, haraji da sauran gudummawa, tare da shirya hanyoyin tara kuɗaɗe, neman tallafi da tsara harkokin kuɗin ƙungiyar.
Kwamitin Ayyuka da Ci Gaba zai gano tare da kula da ayyukan da za a gudanar domin bunƙasa tsohuwar makarantar, tare da haɗa kai da hukumar gudanarwar makarantar.
Sauran kwamitocin kuma za su mayar da hankali kan tattara da adana bayanan mambobi, shirya tarukan sada zumunci da nishaɗi, yaɗa labarai, harkokin shari’a da bitar kundin tsarin mulkin ƙungiyar, ilimi da jagoranci, samar da damar kasuwanci da zuba jari, da kuma tattara tare da haɗa mambobin ƙungiyar da ke zaune a ƙasashen waje.
