Daga MUAZU HARDAWA a Bauchi
An samu tashin hankali yayin zagayen bikin Mauludin Annabi Muhammad (SAW) da aka gudanar a garin Bauchi da kewaye, inda wasu matasa uku suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren daba da wasu bata gari suka kai musu.
An gudanar da zagayen Mauludin ne a ranar Talata, 25 ga Agusta, 2026, wanda ya yi daidai da 12 ga Rabi’ul Awwal, 1448 bayan Hijira. Taron ya samu halartar dubban mutane daga sassa daban-daban na Jihar Bauchi da wasu jihohin Nijeriya.
Duk da armashin da aka yi wa zagayen Mauludin, lamarin ya samu tangarɗa bayan da wasu bata gari suka shiga cikin taron tare da aikata ta’addanci, lamarin da ya yi sanadin mutuwar matasa uku.
Babban Mai Ba Gwamnan Jihar Bauchi Shawara kan Harkokin Addini, Sheikh Aminu Mai Sule Zirami, shi ne ya bayyana hakan lokacin da ya jagoranci tawagar gwamnatin jihar zuwa gidajen iyalan waɗanda suka rasu domin yi musu ta’aziyya.
Sheikh Zirami ya ce bayan aukuwar lamarin, gwamnati ta samu bayanai daga hukumomin tsaro, inda Gwamnatin Jihar Bauchi ta yi Allah-wadai da abin da ya faru tare da addu’ar kada irin haka ya sake faruwa a nan gaba.
Tawagar gwamnatin jihar ta kai ziyarar ta’aziyya ne a madadin Gwamna Bala Mohammed da mai ɗakinsa, Hajiya Aisha Lami Bala Mohammed, kasancewar suna wajen jihar.
Tawagar ta ƙunshi Sheikh Aminu Mai Sule Zirami, Babban Mai Ba Gwamna Shawara kan Harkokin Addini; Malam Ibrahim Na’ibin Liman na Masallacin Ajiyan Bauchi kuma shugaban ƙungiyar makarantun Islamiyya ta Riyala a Jihar Bauchi; Hajiya Aisha Abubakar Amira, wakiliyar mai ɗakin Gwamna; Hajiya Fatima Abdullahi da sauran jami’ai.
Wakilan gwamnatin sun nuna alhininsu kan lamarin tare da tabbatar wa iyalan mamatan cewa gwamnati za ta ɗauki matakin da ya dace domin hana sake faruwar irin wannan lamari a nan gaba.
Sun kuma isar da saƙon ta’aziyya da jajantawar Gwamna Bala Mohammed da mai ɗakinsa ga iyalan mamatan, tare da ba su haƙuri da alkawarin sanar da hukumomin da abin ya shafa domin a gudanar da bincike da kuma hukunta duk wanda aka samu da hannu a kisan.
ɗaya daga cikin waɗanda suka rasu shi ne Hasan Bala Sani, ɗalibi a Kwalejin Koyon Aikin Kiwon Lafiya ta Health Technology da ke Ningi. Rahotanni sun ce matashin ya samu rauni sakamakon soka masa wuka daga wani mutum yayin da yake cikin jama’ar da ke kallon zagayen Mauludin.
Mahaifin marigayin, Alhaji Salisu Bala Sani, ya bayyana cewa ɗansa yana makaranta a Ningi, kuma tun da farko ya ce masa kada ya zo Bauchi saboda suna cikin lokacin jarabawa.
Sai dai ya ce saboda kiran da abokansa suka riƙa yi masa domin ya zo kallon bikin Mauludin, daga bisani Hasan ya amsa kiran nasu da nufin zai koma makaranta bayan sun kammala kallon taron.
A cewar mahaifin, marigayin Hasan Bala Sani ya yanke shawarar kai ziyara gidan kakansa da ke kan Titin Wunti bayan kammala zagayen Mauludin, amma a hanyarsa ne ya gamu da wasu bata gari waɗanda suka soke shi da wuka, lamarin da ya yi sanadin rasuwarsa.
Rahotanni sun nuna cewa ɗaya daga cikin sauran mamatan ya fito ne daga gidan marigayi Sheikh Aminu Bakin Kura, yayin da aka ce sauran iyalan waɗanda abin ya shafa sun buƙaci hukumomin da abin ya shafa su ɗauki tsauraran matakai domin hana sake aukuwar irin wannan mummunan lamari.
Tawagar gwamnatin jihar ta yi addu’ar Allah Ya jikansa da sauran waɗanda suka rasu, Ya gafarta musu kurakuransu, Ya sanya Aljanna ta zama makomarsu, tare da bai wa iyalansu haƙuri da juriyar wannan babban rashi.
Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da hukumomin tsaro ke ci gaba da ƙarfafa matakan hana aikata laifuka a Bauchi, musamman a lokutan tarukan jama’a da bukukuwan addini.
