30
Apr
Duk da matsayin da jihohin yankin Arewacin Nijeriya suka samu kawunan su a cikin shekaru 16 da su ka shuɗe har zuwa yanzu da gwamnatin APC ke mulkin ƙasar, alamuran yankin suka shiga taɓarɓarewa, harkar tsaron rayuka da dukiyoyin al'umma ya kau, kusan kowane ƙauye su na fama da ruɗani masu garkuwa da mutane, don amsar kuɗin fansa, su na fama da hare-hare da rigingimun makiyaya. Gwamnonin da haƙƙin hakan kuma ya rataya a wuyan su ba su taɓuka ba, don ɗaukar wani mataki, walau na gaggawa ko wanda aka tsara na musamman, don magancewa. Haka nan su na ji,…