Tsaro: Gwamnonin Arewa na da rawar takawa

Duk da matsayin da jihohin yankin Arewacin Nijeriya suka samu kawunan su a cikin shekaru 16 da su ka shuɗe har zuwa yanzu da gwamnatin APC ke mulkin ƙasar, alamuran yankin suka shiga taɓarɓarewa, harkar tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma ya kau, kusan kowane ƙauye su na fama da ruɗani masu garkuwa da mutane, don amsar kuɗin fansa, su na fama da hare-hare da rigingimun makiyaya.

Gwamnonin da haƙƙin hakan kuma ya rataya a wuyan su ba su taɓuka ba, don ɗaukar wani mataki, walau na gaggawa ko wanda aka tsara na musamman, don magancewa. Haka nan su na ji, su na kuma gani aka yi ta fatattaka yankin Arewa, ana haddasa rigingimu da fitintinun da su ka rarraba kawunan su, aka kuma janyo wata fitina wai ita Boko Haram, wacce ta ke tayar da zaune tsaye.

A wancan lokacin gwamnonin Arewa sun zamanto tamkar wasu sha-ka-tafi, sun kasa yin magana ko tsawatawa dangane da abubuwan da ke faruwa a yankin su. Hasali ma an sha yin zargin cewa, da su ne ake haɗa baki, ana ba wa ƙungiyar Boko Haram cikakken goyon bayan da ya kai ta ga matsayin da ta buwayi kowa. Wasu na cewa wasu gwamnonin ne ma da kan su ke jagorantar ƙungiyar Boko Haram ɗin a ɓoye, kuma hakan ne ya sa aka gagara kai ta ƙasa cikin ɗan ƙanƙanin lokaci, kamar yadda yanzu ma ake zargin wasu gwamnoni da jami’an tsaron da ke cikin wannan gwamnati wajen kitsa matsalolin masu garkuwa da mutane da sace-sacen dabbobi da dukiyoyin talakawa, kuma su ke amfana da rikicin bisa voyayyar manufofin su na siyasa.

To, amma inda aka fi ganin wallen gwamnonin Arewa da kuma shugabannin ta shi ne, rashin taɓuka su wajen kawar wa Arewar da matsalolin da su ka ƙarfafa taɓarɓarewar tsaro da koma-bayan tattalin arziki sakamakon durƙushewar ɗaukacin masanaantun da ke yankin, kuma hakan ne ya yi sanadiyyar rashin aikin yi ga matasa da magidanta; ya kuma haddasa baqin talauci da mayata ga sauran jamaa.

Gwamnoni 19 na Arewacin ƙasar sun sha hallara a Kaduna su yi taro don gano bakin zaren warware dukkan matsalolin da suka addabi yankin Arewacin ƙasar da kuma dabarun kawo ƙarshen masifar da ƙungiyar Boko Haram ta haddasa da masu garkuwa da mutane, satar dabbobi da ta’addanci a yankin Arewa maso Yamma da faɗace-faɗace manoma da makiyaya a jihohin Benuwai da Taraba.

Gwamnonin a yadda suke nunawa a fuskar su da kuma furtawa da fatar bakin su, wai su na takaicin yadda waɗanda a halin yanzu ke bugun ƙirji, su na tunƙaho cewa su ne manya ko kuma shugabannin Arewa su ka kasa ci gaba da aiwatar da kyawawan manufofin ciyar da Jihar Arewa gaba kamar yadda shugabannin farko su ka assasa, aka kuma ga alfanun haka, aka ci gajiyar su a ƙasar gabaɗaya.

A cewar su babu wani ƙorafi ko kukan-zucin da gwamnonin yanzu za su iya nunawa game da haka, idan har aka yi laakari da yadda Arewar ta komo a halin yanzu. Mafita daga haka shi ne turzawar da shugabanni da gwamnonin yanzu za su yi na sauke nauyin da jamaan su su ka tattaru, su ka ɗoɗɗora masu, su kuma tashi haiƙan wajen biya masu buƙatun su, ba biye wa son zukatan su ko raayoyin wasu can daban ba.

A kowane zubin shugabannin jihohin Arewa, walau na soji ne ko kuma na farar hula, sai gwamnonin su sun ƙirƙiro wata ɗabia ko tsatsubar taro da sunan haɗa kan Arewa don amfanin jamaan ta, kuma duk lokacin da aka yi taron babu wani abin alherin da su ke tsinana wa jamaar su, sai dai su ne su ke amfana, domin tun can farko an tsiri taron ne don a kai ga biyan wata buƙatar gwamnonin su kaɗai.

Gwamnonin Arewa ne kaɗai ke yin irin wannan taron, su na kuma dodorido da sunan Sardaunan Sakkwato, Ahmadu Bello, Firimiyan jihar Arewa na farko, kuma na ƙarshe, amma gwamnonin sauran jihohin sassan ƙasar nan ba su yi, ba su kuma tinƙaho da firimiyoyin jihohin da su ka gabata. To, me ya sa sai a Arewa ne ake yawo da sunan Sardauna idan ana so a yaudari talakawa?

A nan Arewaci gwamnoni sun sha yin taro don shawo kan matsalar Arewa, amma a fakaice wasu su na ganin taro ne kawai na yaudara, tunda tun-tuni sun saba yi wa jamaa gafara-sa, amma har yanzu ba su ga ƙaho ba.

Matakan magance matsalolin Arewa ba su buƙatar yawan taron gwamnonin da su ka zame tarin tsintsiya ba shara, domin gwamnonin su na da halin bin tafarkin da zai tserar da jamaar su daga matsalolin da ke addabar su nan take, domin su ne ke da wuƙa, su ne kuma ke da nama a hannuwan su. Idan har ba su yi amfani da dukiyar talakawan da aka damƙa masu amana ba wajen cire masu ƙangin talauci da fatara, da kuma tashi tsaye wajen haɗa kai da gwamnatin tarayya don magance matsalolin da su ka zame wa yankin kakani-ka-yi tsawon shekaru ba, to ina amfaninsu a gare su? Talakawa su na kallon gwamnonin jihohi su ne babbar matsalar Tarayyar Nijeriya tunda sun kasa cire masu kitse a wuta.

An sha jin cewa za a magance illolin barace-barace, da rashin aikin yin da ya zame ruwan dare a jihohin Arewa, amma duk a banza, maimakon gwamnatin ma ta zage damtse wajen nemo dabarun magance hakan, sai kuma ta nemi yin kiɗa bashi kuma za ta ɓata rawar ta da tsalle, wajen dulmiya mabaratan mummunar hanyar da ta fi barace-baracen illa.

Domin har yau ɗin nan jamaar jihohin Arewar ce dai ke yawon bara a faɗin tarayyar Nijeriya, ana ta kyarar su duk inda su ka kukkurɗa.

Masanaantun Arewa kaf sun durƙushe, an kuma yi watsi da aikin gona, jamaa na ta shiga bariki aikin ci-rani, wasu na faskaren itace, wasu na ga-ruwa, wasu na yankan farce, wasu na sayar da fetur ko baqin mai, wasu na yin dako da tura baro, wasu na sayar da jaridu, wasu kuma na gararamba a tituna, ba aiki sai ragaita ko zauna-gari-banza.

Jahilci da cututtuka sun fi yin katutu a yankin Arewacin ƙasar, alhali kuwa dukiyar jihohin Arewa na da matuƙar tarin yawa, kuma ba mai amfana daga gare ta sai shugabanni da yan barandar su. Wai shin ma su waɗannan gwamnonin da su ke fafutikar farfaɗo da martabar Arewar da su ka ce magabatansu sun banzartar, za su kwatanta halaye irin na mazan jiya?

Shin a yanzu haka su na nufin ba su san cewa, hatta magunguna a asibitoci ko kayayyakin tiyata (wato fiɗar marasa lafiya) babu ba sai dai talakawa su yi ta ɓara a gidajen rediyo da talbijin kafin su samu ɗan abin da za a yi masu magani a asibitocin da su ke cewa gwamnatocin da magabatan su su ka karɓi milyoyin Nairori, don kulawa da lafiyar jamaar su a banza? Baicin haka nan wacce dabarar haɗin gwiwa za su iya yi, don tayar da masanaantun da su ka duddurƙushe da siraɗansu cikin ƙiftawa da bisimilla?

Kodayake dama wasu na yi wa gwamnatin kallon cewa, duk kanwar ja ce, ja ya faɗo ja ya ɗauka ne, ba a rabu da Bukar ba an haifi Habu, duk halayyar su guda, ɗabi’un su iri ɗaya, ba su da bambanci sai bambancin jam’iyya, amma da waccan gwamnati da aka hamɓarar da kuma wannan kamar Ɗanjuma ne da Ɗanjummai.

An daɗe dai ana shan yan Arewa, kuma har yanzu ba su warke ba, amma sai dai sun ƙudurta aniyar cewa ba za su sake yarda gwamnoni da shugannin su su ci gaba da rarraba kawunan su, ko a yaudare su ba, domin an yi dogon dare, gari kuma ya waye. Gwamnonin Arewa su na da rawar takawa don magance matsalolin da su ka yi wa yankin dabaibayi amma sun ɓuge da dogon barci.

Ka da a manta, ku san shika-shikan zaɓar wannan gwamnati shi ne don ta magance wa talakawan ƙasar nan matsalar tsaron da ta samo asali daga ƙungiyar Boko Haram, wadda ta kafa sansani a Arewa maso gabashin ƙasar nan, kuma su ke kai hare-hare a kasuwanni da wuraren ibadu.

Abinda ya tilasta wa jama’a neman canji kusan ko ta halin ƙaƙa, su na ganin watakila a samu sauki. Sai ga shi bayan nasarar gwamnatin APC sai harkar tsaron ta ɗauki sabon salo ta fuskoki da ɓangarori mabanbanta; kama daga garkuwa da mutane, kisan gilla da satar dukiyoyin jama’a da ‘yan fashin daji ke yi.

‘Yan bindiga sun raba ɗaruruwan mutane da muhallin su, sun mayar da dubban yara marayu, inda matan aure su ka koma zawarawan ƙarfi da yaji. Noma ya gagara a wuraren da matsalar tsaro ta yi ƙamari, yanzu ta abinda za a noma a ci ake yi ba wanda za a kai kasuwa domin biyan buƙatar kai ba.

Daga ƙarshe ya kamata Gwamnatin Tarayya da na jihohi, waɗanda su na da gagarumar rawar da za su taka wajen magance matsalar tsaron nan, da su ƙara zage damtse da bayar da ƙaimi wajen share hawayen talakawan da su ka zazzaga musu ƙuri’u har su ka kai ga matsayin da su ke kai yanzu.