Inuwa Ibrahim Waya da tsatsonsa a mahangar tarihi: Kaza da tone-tone?

Daga KWAMRED IBRAHIM ABDU ZANGO

Siyasa wata aba ce wacce ake yin ta domin kyautata wa al’umma a kowacce ƙasar duniya, wacce ake yin zaɓe, domin mulki irin na zamani. Gaskiya kamar yadda tarihi ya nuna an fara salon wannan mulki tun tale-tale, kususan a can wata ƙasa wacce ita ce farkon bayyanar Turawan duniya. Haka dai abin yake kuma a wancan duniyar Turawa wacce ita ce ta buɗewa dukkan duniya harkar dimukraɗiyya, wacce yanzu ta haɗe duniya kaf ɗinta.

Duk da cewa waccan ƙasa ita ce farko, amma mun karanta tarihinta a makaranta wadda har rumawa suka rungume ta ko da kuwa mulkinta irin na sarautar gargajiya ne, yanzu cikin wannan ƙarnin wadda har Amurka yanzu ita ce uwa makarɓiya ga wannan hanyar mulkin siyasa.

Gaskiya vatancin juna akwai shi cikin siyasar duniya a yau wanda har kashe-kashen abokan gaba ake yi kamar J.F. kennedy da sauransu. Babban abin baƙin ciki shine ɓata suna da faɗin abubuwan da ba gaskiya kurum, domin a kautar ga masoya da wanda suke so. Haka lamarin siyasa yake a duniya kaf ɗinta.

Na ke ganin siyasar Nijeriya ta ɓaci ne tun shekarar 1963, inda aka riƙa ƙone-ƙone kawai, domin wani sashi na ƙasar nan bai sami biyan buƙatar sa ba ta kafa gwamnatin tarayya. Mu kuma an ce akwai lokacin da aka riƙa yawo da ɗan akuya mai gemu har ƙasa ake danganta shi da wani hamshaƙin waliyin siyasa, haka abin ya kasance daga shekarar 1960 zuwa 1966; kowa ya san kyakkyawar rawar da shugabannin Nijeriya na wancan lokaci suka yi, amma sun gamu da sharri iri-iri har Allah Ta’ala ya ɗauki ransu cikin wani hali na ‘yan ta kife, Allah Ya jiƙan ’yan siyasarmu na 1966 zuwa 1979 zuwa 1984.

Mun yi musu addu’a ne ganin yadda suka yi ƙoƙarin cure Arewa su zama jama ɗaya, alu’umma ɗaya, duk da yake an sami wasu sun fitsare kansu domin ruguza wannan babbar ƙasa ta arewa mai ƙasar albarka ta noma da ma’adanai masu yawan gaske.

Na san dai a da babu irin wannan mummunar ɗabi’a ta cin mutuncin wasu, a wani lokaci da ya shuɗe an yi hoton kan jaki aka ce na wani jigon shugaba ne wanda Allah yayi masa wata baiwa ta son talakawa. Haka ya mutu da son jama’ar Nijeriya kuma su maƙiya suna nan a duniya, kuma abinda Allah ya ƙaddara musu na shugabantakar ƙasa suna nan suna ta lalibe, Allah shine masanin izaƙar siyasarmu, sai dai ta kawo ƙone-ƙone a wannan jiha ta Kano kuma wai da sunan siyasa, kai abin akwai kaico.

To, na share filin ne domin na faɗa wa ’yan kamashon siyasa cewa, ba yanzu sheɗancin siyasa yake yi wa mutanen kirki cikas ba, wato an daɗe cikin wannan makauniyar siyasa wacce ko badaɗe ko bajima, matuƙar ba mu bar ɓatanci ba, to za a ɗauke mu kawai jahilai waɗanda basu san komi ba.

’Yan kwanakin nan na fahimci akwai wani bawan Allah wai shi Barista Inuwa Ibrahim Waya, wanda ya nuna buƙatarsa ta shiga siyasa, wadda babu wani mahaluki da zai hana wani shiga siyasa, domin ba gadon gidansu ba ne. Saboda haka kowa yana da ikon shiga rigar siyasa kususan ga mai ilimi shine fitila haskaka duniya.

Na fahimci cewa shi wannan mutum, wato Inuwa Ibrahim waya (Barista) mutum ne da ya fito daga gidan ilimi ganin danginsa ɗaka da waje duk masu ilimi ne na arabiyya da kuma na zamani.

Bari ka ji; shi Inuwa Ibrahim jika ne ga babban direban sarkin Kano, marigayi waliyyin allah Sir. Muhammadu Sanusi (1953 zuwa 1963). Kuma idan ban manta ba, ana kiran sa Madugu, sannan akwai Farfesa Mijinyawa da Tijjani Isma’il da kuma Alhaji Sule waya da alhaji Iro Waya, waɗannan ko shata na Yalwa sai da ya yi musu waƙa kususan don dangantakarsu da babban birni mai tarihi na Gaya, Gayyar Daraja, dukkaninsu kawunai ne ga shi wannan Barista kuma mutane ne da suka fito daga gidajen sarauta na Gaya Uwar Gayya, wacce ita ce ta kafa Kano, kamar yadda Amirigo Basfucci ya samar da Amurka ya kuma laƙaba mata suna amurka da sunansa na farko, wato amirigo Basfucci!

Ita Kano sannan wannan murumin Gaya ne kuma sunansa Kano, wacce yanzu Inuwa Ibrahim Waya yake nema wurin allah. Kuma wayar nana ake faɗi fili ne tsakanin asibitin Murtala zuwa sashen kurawa har ya shiga durimin Iya unguwar da ɗaya ce tilo wurin wayewar ’yan siyasa na gidi bana jabu ba.
Duk wasu manyan ’yan siyasa suna nan cikin Durumin Iya, ɗauki masu daraja Alhaji inuwa wada da Marigayi Alhaji Sule Gaya, su Alhaji Labaran Tanko da sauransu, Allah Ya ji ƙan su ya kuma gafarta wa wadannan bayin Allah, amin.

Mai karatu kada ka ɗauke ni irin su wa’e, a’a gani na yi wasu suna son canza niyyarsu ta barin gaskiya. inuwa Ibrahim Waya ɗan dangi ne gaba da baya, idan yana son shiga siyasa, “he is welcome warmly”.

Kwamred zango ya rubuto ne daga birnin Kano a Jihar Kano da ke Nijeriya. Za a iya samun sa a wannan lamba; 08175472298.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *