Ina mafita ga matsalolin Arewa?

Daga AMINU ƊANKADUNA AMANAWA

Arewa yanki ne daga cikin yankunan dake akwai a dunkulalliyar kasa da turawan mulkin mallaka suka hade yankunan kudu da Arewa waje daya da yanzu muke a ciki da kuma tinkaho da ita ta Nijeriya.

Duk da yake ko a arewar ta kasu a yankuna daban-daban, kama daga arewa maso gabas, yamma, dama tsakkiya, yankin na fuskantar kalubalai da tarin matsalolin dake kokarin mayar da yankin saniyar ware.

Matsalolin da suka tashi daga talauci da kusan ke akwai a lunguna da sako na jihohi, zuwa na tsaro da ya zama ruwan dare, garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, rashin ayukkan yi, da kuma karancin ilimi da samar da abubuwan more rayuwa, duk kuwa da cewa yankin na da tarin kasar noman da ita kanta idan an dogara da ita zata share kusan dukkanin hawayen matsalolin da yankin ke fuskanta.

Iyaye da dama sun rasa ‘ya’yan su, yayin da mazaje suka rasa matansu, mata sun zama zawarawa, baya ga marayu da tarin yara suka zama a sanadiyar matsalar tsaro dake addabar yankin, musamman ta Boko Haram a arewa maso gabashin kasar nan, da kuma wacce yankin arewa maso yamma ke fuskanta na kai hari a kauyukkan da ba su ji ba su gani ba, garkuwa da waɗanda abin sakawa bakin salatin ma neman gagarar su yake, ga kuma rikicin Fulani makiyaya da manoma da kusan alaƙar suke ta a waje ɗaya, kamar a ce ɗan jumma da ɗan jummai ne, amma rikice-rikicen da ake yawan samu a wasu lokutta nan da can na son shafe wannan dadadden tarihin.

Tarin matsalolin da ke ci gaba da faruwa a yankin Arewa, ya sanya gamayyar mawaƙa da dama na Arewacin Nijeriya shirya waƙar da suka yi wa take da “Arewa Mu Farka” waƙar da a cewar su sun shirya ta ne domin bada tasu gudunmawa wajen janyo hankali da farkar da mutane a kan matsalolin da suke addabar al’ummar Arewacin Nijeriya.

A waƙar da ta haɗa mawaƙa a ɓangarori daban-daban na Arewacin Nijeriya, mawaƙan sun baje manya da ƙananan matsalolin da suka addabi yankin Arewacin Nijeriya.

Wanda a ƙarshe suka nusar da shuwagabannin da Allah ya albarkaci yankin da su kama daga shugabannin siyasa, sarakuna, attajirai, dama talakawa akan hanyar da ya kyautu kowa ya bi wajen tashi daga dogon barcin da muke a Arewacin Nijeriya, wajen kawo ƙarshen tarin matsalolin da suka zame mana tarnaki wajen samun cigaban da yakamata yankin a ce ya sama.

Dama dai masana da masu lura ko sharhi kan lamurran yau da kullum, a kullum na ci gaba da dasa ayar tambayar wai meke damun mutanen Arewar ne?

Bayan duk abin da yanki ke buƙata wajen samar da cigaba, Allah ya albarkaci Arewacin Nijeriya, kama daga shuwagabannin da ke riƙe da madafun iko daban-daban a gwamnatin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, amma abin damuwa da ban haushi har yanzu babu hoɓɓasar da suke na kawo ƙarshen wannan matsalar da ke cigaba da kassara yankin Arewacin ƙasar nan, baya  ga ƙasar noma da rashin tsaron ya jefa fargaba a zukatan manoma da ke noman kasuwanci, dana samun abin ci maka domin cigaba da rayuwa a doron wannan duniyar.

Irin wadannan matsalolin matukar ba’a dauki matakar kawar dasu ba, to ba makawa kamar yanda masana ke bayyanawa yankin Arewa zai ci gaba da kasancewa abin tausayi musamman ma talakawa da marasa karfin dake yankin na arewacin najeriya.

Matakan kuwa da ya kyautu ace masu riƙe da madafun ikon sun dauka su ne; haɗa kai waje ɗaya domin ba ta yanda matsalar tsaro za ta yi nasarar a kawar da ita ba tare da samun haɗin kan masu ruwa da tsaki a yankin ba, kama daga sanatoci, ‘yan majalisar tarayya, gwamnoni da ke yankin, ta hanyar ajiye bambancin siyasa, ko addini idan aka zo kan maganar da ta shafi ciyar da yankin a gaba.

Mu duba yanda a kwanan nan ‘yan majalissar wakilai da suka fito daga yankin Niger Delta, suka ajiye bambancin siyasa wajen buƙatar Gwamnatin Tarayya ta bai wa yankin kuɗaɗen da ake zargin Ibori da warewa da ta karɓo a ƙasashen ƙetare da a cewar su ba mallakin Gwamnatin Tarayya ba ne.

Ga kuma na tsayin dakar da jami’an da ke yankin suka yi na ganin cewa an biya diyyar waɗanda cin zarafin jami’an Rundunar Sars ya shafa.
Mu me ke damun mu ne? Me ya sa ake samun ƙarancin haɗin kan? Idan ana tafiya hakan kowa tasa na fisshe sa kuwa?

Waɗannan da tarin tambayoyin nasan na a zukatan masu kishin Arewa da kuma kawo ƙarshen matsalolin da ke addabar Arewacin Nijeriya.

Me ya sa gwamnonin mu ba za su ajiye bambancin jam’iyya, siyasa ko addini a tunkari waɗannan matsalolin? Ina ‘yan Majalisar Dattawa da na wakilai duk shiga lungu da saƙo na mazaɓun su lokacin zaɓe na ganin cewa an zaɓe su domin kare muradin yankunan su?

Talakawa me kuke jira wajen dukufa addu’oin kawo ƙarshen matsalar?
Tabbas idan har aka samu haɗin kai na shugabannin siyasa, sarakuna, jami’an tsaro, talakawa to tabbas kwalliya za ta kai ga biyan kuɗin sabulu a irin waɗannan matsalolin da ke damun Arewacin Nijeriya, Arewa ta koma yadda take ada kamar yadda Sardaunan Sakkwato, Sir Ahmadu Bello, da su Malam Aminu Kano, Tafawa Ɓalewa, suka ɗora tubalan ciyar da yankin gaba.

Amanawa Ɗan Jarida ne a Sokoto. Za kuma a iya samun sa a imel; [email protected]