Me ya sa soyayya ke mutuwa bayan Aure?

Daga AMINA YUSUF ALI

Kamar yadda muka sani ko muke iya gani, yawancin aurarrakin yanzu ana dasa su ne bisa soyayya. Wannan abu haka yake musamman a al’ummar Hausa. Da shuɗewar zamani da ilimi har ma da wayewa sun sa an kusa ma a manta a ana auren dole. Amma abu mafi mamaki shi ne, bayan an yi auren soyayyar wacce kamar a haɗiye juna. Sai kuma wasu abubuwa na rashin jituwa su vullo, a rasa ma gane kan zaman nasu. A haka idan ba a kai zuciya nesa ba, sai rabuwa. Ko kuma idan ba a rabun ba, a yi ta zaman ba daɗi. Wani lokacin ma har abun ya shafi alaƙar da ke tsakanin danginsu. Idan ma auren zumunci ne, zai iya lalata zumunci.

Na san mai karatu ba zai kasa samun labarai a kan hatsaniyar aurarraki, wacce ta sha kai wa ga ɗaya ya ɗauki ran ɗaya ba ko makamancin haka. Kuma da za ka bi diddigin irin wannan za ka ga aure ne na ka-so-na-so.

Amma abin mamakin shi ne, ta yaya aka haihu a ragaya? Wato ta yaya har so zai juye ya koma ƙiyyaya mai zafi haka? Wasu dalilan da nake ganin za su iya haifar da hakan sun haɗa da;

  1. Rashin yin soyayya da aure tsakani da Allah:
    Hausawa na cewa so hana ganin laifi. Idan mace da namiji suna son juna don Allah, sukan zama masu yawan yi wa juna uzuri tare da juriyar zaman tare. Amma auren da aka xora shi bisa sha’awa, to fa bayan an yi aure.
  2. Zato:
    Shi ne ɗora aure a kan igiyar zato. Wato a dinga hangen kamar wanda ko wacce za a aura suna da wani abu na musammaan. Bayan an yi auren idan ba a samu abinda ake so ba, sai kuma a fara hango laifin juna komai ƙanƙantar laifi sai a mai da shi babba. Ma fi yawan lokuta ma, sai a nemi soyayyar a rasa. Haka idan ba a ci sa’a ba ma, abu na iya girmama ya zama babbar matsala sosai.
  3. Rashin fahimtar juna kafin a yi aure: Yana daga hikimar Musulunci da kuma al’adar Bahaushe saurayi da budurwa su ɗan samu lokuta su dinga tattaunawa don fahimtar juna kafin aure. Wannan yana ƙara ƙulla soyayya da shaƙuwa mai ɗorewa tsakaninsu. A nan suke fahimtar abinda kowa yake so, da wanda ba ya so. Rashin fahimtar juna ko fahimtar bai-bai yana jawo matsala a aure. Kuma yana jawo soyayya ta daƙile.
  4. Rashin haƙuri:
    Rashin haquri ma babar matsala ce da take jawo naqasu a soyayyar ma’aurata. Miji ko mata ba Annabawa ko mala’ku ba ne. Su ma mutane ne kamar kowa. Suna yin kuskure. Ya kamata ma’aurata su koyi yafe wa juna. Ba dukka laifin da aka yi maka a gidan aure za a ce wai dole sai an rama ba. Wani lokacin daga ramuwar matsaloli suke ƙara ta’azzara. Kuma haƙuri ba na mace ba ne kaɗai. Nasu ne dukka.
  5. Rashin uzuri:
    Kamar yadda aka faɗa a sama, miji ko mata ‘Yan Adam ne kuma ajizai ne. Doke sai da uzuri. Kamata ya yi idan wani ya aikata wa wani ba dai-dai ba, a yi masa uzuri. Ta hanyar duba kyawawan abubuwan da ya yi a baya. Yi wa abokin zama alƙalanci a kan duk wani ƙaramin kuskurensa zai sa ya ji an yi masa rashin adalci, kuma ba a neman alkhairinsa. Hakan zai iya haifar da rashin yarda a zuciyarsa. Hakan kuma zai dusashe soyayyar su.
  6. Rashin girmama magabata da dangi:
    Shi aure ba tsakanin mace da namiji ne ba kawai. Ya haɗa har da dangoginsu. Rashin girmama iyaye da wulaƙanta dangin mutum yana sa soyayyarsa ga mutum ta dakushe gabaɗaya.
  7. Larya ko yaudara:
    Idan ɗaya daga cikin ma’aurata ya yi wa ɗaya ƙarya, to, idan aka yi aure aka zo zaman gaskiya da gaskiya kuma ɗayan ya gane, hakan zai zubar masa da ƙima. Kuma dole wanda aka yi wa ƙaryar zai ga an munafunce shi, kuma an ci amanarsa/ta. Misali namijin da zai auri mace ya yi mata ƙaryar gidansa ne daga baya ta gano haya yake yi. Hakan zai iya raunata soyayyarta gare shi.
  8. Rashin girmama aboki/abokiyar zama da ƙasƙantar da shi: Shi ma yana kawo naƙasu a soyayya.
  9. Ɗaukar zuga:
    Wato ɗaukar zuga daga dangi ko abokai da ƙawaye da sauransu. Wannan babban kuskure ne da ma’aurata suke tafkawa. Kuma ya fi faruwa a vangaren namiji. Maimakon shi da ya auri matar shi ne zai tsaya ya fuskanci halayenta kuma ya fi saninta fiye da kowa. Don ya fi kowa kusanci da ita. Amma sai ka