Akwai bambanci ƙwarai tsakanin rubutun zube da na jarida – Mairo Muhammad Mudi

*Ba na zayyana labari irin na abinda ake cewa ‘mijin novel’- Mairo Mudi

Daga AISHA ASAS


Sanannen abu ne marubuta sun karkasu daban-daban, inda za ka samu wani ya fi ƙwarewa a rubutun waƙe, ko zube ko kuma wasan kwaikwayo da sauran su, duk da haka akwai wasu tsiraru daga cikin marubuta da aka ba su baiwar shiga kowane ɓangare na Adabi su taka rawar da za a yaba masu. Irin waɗannan marubuta dai su na
da karanci domin ba kasafai ake samun su ba. Waɗannan marubuta sun kasance gwanaye a kowane ɓangare na rubutu har a kasa gane wane fage su ka fi ƙwarewa a kai. Mairo Muhammad Mudi na ɗaya daga cikin waɗannan marubuta, domin gwana ce a rubutun zube tun daga na turanci har zuwa na Hausa, haka zalika ta shahara kwarai a ɓangaren rubutu na muƙala, har ta kai matakin edita a aikin jarida. Ku gyara zama don jin tataunawar mu da Mairo Muhammad Mudi:

Mu fara da jin tarihin ki.
An haife ni a Suleja, na yi firamare a Suleja, na yi ƙaramar sakandire a GGJSS Sabon Wuse Jihar Neja, na yi babbar sakandire GGSS Dutse, Abuja. Daga nan na yi ‘Suleja Academy’ na zo na tafi Kaduna Polytechnic inda na fita da ‘National Diploma’ a ‘Mass Communication’. Na tafi jami’ar Abuja inda na karanta ‘Sociology’ a matakin digiri na farko. Daga nan na yi aiki a NTA Abuja, sannan na yi aure a 1997. Bayan nan na sake aikin wucin-gadi a NTA Minna. Na kuma zama wakiliyar Leadership Newspaper a Minna kafin na dawo ofishin su da ke Abuja na ci gaba da aiki. Yanzun haka ina aiki da sashen kula da walwalar ƙananan yara na ma’aikatar mata da ke Jihar Neja. Kuma ina tafiyar da gidan jarida ta yanar gizo mallaki na kuma ina da wata kungiya mai zaman kanta mai yaƙi da cin mutuncin yara da mata. Na yi aure a 1997, Allah Ya albarkace ni da yara.

A kwanakin nan ki ka kaddamar da littafin ki na ‘Sarƙaƙiya’. Shin ina labarin ya samo asali?
Labarin ‘Sarƙaƙiya’ ya samo asali ne kawai a tunani na inda na ke sha’awar ganin malamai su na kyautata wa ɗaliban su tare da ganin iyaye sun kula da haƙƙin da Allah Ya ɗora masu inda in aka samu saɓanin haka, za mu kasance masu nadama.

Kafin ki fara rubutun zube, kin kasance ‘yar jarida. Ko akwai bambanci tsakanin rubutun biyu?
Akwai bambanci ƙwarai da gaske. Rubutun aikin jarida ya ta’allana ne a kan zahiri, kan abun da ya faru za ka faɗa ba tare da ƙari ko ragi ba. Kuma ka kasance mai adalci ga dukkan ɓangarorin da ka ke ba da labari akai, ma’ana kar ka sa ra’ayin ka ko kuma nuna ka na tare da ɓangare ɗaya, dole ka zama adali don ka samu nasara akan aikin jarida. Amma rubutun zube ya fi maida hankali a kan ƙirƙira. Mai rubutu ke da wuƙa da nama game da dukkan waɗanda ya ke ƙirƙira a labarin sa. Shi ke jan akalar rayuwar waɗanda ya ke rubutu a kai.

Kafin fitowar ‘Sarƙaƙiya’ ko akwai wani littafi da ki ka wallafa?
Kafin fitowar Sarƙaƙiya akwai littafai wajen goma amma yawancin su na Turanci ne. Sarƙaƙiya shi ne littafi na biyu da na rubuta da Hausa, na farkon akwai ‘Tun Ran Gini’.

Marubuta da dama sun daina fitar da littafai dalilin rashin ciniki, sai ga shi a cikin irin wannan yanayi kin fitar da littafi. Ko ya aka yi ra’ayin ki da na saura ya bambanta?
Ki rabu da sha’awa. Wato abinda Bature ke cewa ‘passion’. A gaskiya rubutun littafi in ki na jiran masu saya ne don ki samu riba ko ki yi kuɗi, to ki manta kawai! Amma ni tun farko na ɗauki rubutu ko littafi hanya ce ta isar da saƙo wanda na ke ganin shekaru dubu nan gaba zai iya yin tasiri, In Sha Allah. Saboda ina rubutu ne don wannan zamani, idan sun ƙi kula da rubutu na ina da yaƙinin cewa zuwa gaba wasu zai amfane su ko bayan raina.

Me ya sa ki sha’awar zama marubuciya?
Don na isar da saƙo kuma na fi bayyana abinda ke cikin raina ta hanyar rubutu. Zan iya magana ta minti goma in rasa abinda da zan faɗa amma in ki ka kyale ni da rubutu a zaune zan iya zayyana maki shafuka 100 ban ƙure tunanina ba.

Ta ya ki ke ganin za a iya fito da harkar rubutu daga kwazazzabon da ta faɗa?
Dole ne gwamnati ta bai wa marubuta ƙwarin gwiwa da tallafi da kasancewa su na ingiza mutane na karatun littafan mu. Yin haka zai ba marubuta ƙwarin gwiwa.

Littafin ‘Sarƙaƙiya’ labarin gaske ne ko ƙirƙirarre?
Ƙirkirarren labari ne.


Da yawa a makaranta su na ƙorafin rashin ƙalailace rubutu kafin ɗab’i a kaso mai yawa na littattafai, sai ga shi littafin ‘Sarƙaƙiya’ ya fito da tsari irin wanda masu karatu ke muradi. Shin ko akwai wata hanya da ki ka bi wadda wasu daga cikin marubuta ba sa bi?
Ni rubutu na na kan zayyana abinda in dai mutum ya na karantawa zai ɗauka da gaske ya faru ba labari ne da za ka ce wannan ba zai taɓa faruwa ba. Labarai na dole ne ka ganka ciki ko wanin ka. Ƙirƙira da ni ke ya na tare da abubuwan da ke faruwa ne. Kuma ba ni yanke layin labari na wanda in mutum na karantawa ba zai so ya ajiye ba har sai ya kai ƙarshe. Ba ni zayyana labari irin na abinda ake cewa ‘mijin novel wanda ba a taɓa samun sa ko kuma soyayya da ba za ta taɓa zama zahiri ba.

A ɓangare ɗaya kin kasance ɗaya daga cikin jajirtatun mata da ke amfanar da al’umma ba ta ɓangare guda ba. Shin ya aka yi ki ke iya tauna taura biyu a lokaci ɗaya, ma’ana rubutu da aiki?
Babu wani abu na daban, kawai dai in ka na da ra’ayi a abu dole ka nemi wa wannan abun muhallin sa a rayuwar ka. Ba ni wasa da zancen aure na da tarbiyyar yara na gaskiya amma wannan bai hana ni bai wa abubbuwa masu muhimmanci a rayuwa ta lokaci da ya dace ba. In ka na shirya komai a harkokin rayuwar ka za ka ga sauƙi; kana in ki na da mijin da ya fahimce ki ya ke karfafa maki gwiwa har wata rana ya taimaka maki kan burin ki ya cika komai zai zo da sauƙi. Miji na ya kasance mai fahimta ya na ba ni ƙarfin gwiwa tare da taimaka mani wajen ganin na samu nasara a kan abinda na sa gaba. In dai zancen yara ne sai inda karfin sa ya kare zai shigo ya ga ya taimaka wajen ƙwato masu haƙƙinsu. In marayu ne na kawo gida zai karɓe su ya ba su kulawa da sunan sa. Bai bambanta su tsakanin ‘ya’yan shi da na su.

Wace shawara za ki ba wa marubuta da su ke tasowa yanzu?
Su tabbatar sun rubuta komai su ajiye, kar abubuwan kamar rashin tallafi da karfafa gwiwa ya sa su juya wa burinsu baya. Wata rana za su ga alheri da ke tattare da rubutu. Dole ne su jajirce don cimma burin su.

Mene ne muhimmancin samar da ingantaccen rubutu ga al’umma?
Rubutu na da muhimmanci domin shi kan shi koyarwar tarihi, addini, kimiyya da fasaha da sauran su ba su da fa’ida in ba tare da an rubuta ba. Saboda haka muhimmacin rubutu ba zai iya zayyanuwa a zama guda ba don ilimi kan shi ya jingina ne a kan rubutu.

Wane buri ki ke da shi a ɓangaren rubutu?
In ga rubutu na ya shiga ko’ina a duniya. Mataki na farko shi ne ina da burin in ga an amince da littafai na a makarantu da ɗakunan karatu na ƙasar nan.

Wane lokaci ki ka fi sha’awar yin rubutu?
Yawanci in na tsinci kai na a halin damuwa, na fi rubutu gaskiya. Maimakon in zauna ina zullumi sai in ɗauki rubutu kawai ina ta yi har Allah Ya kawo mani nutsuwa.

Daga ƙarshe wane kira za ki yi ga marubuta ‘yan’uwan ki?
Ba zai wuce in ce masu su jajirce ba don kuwa duk da muhimmacin rubutu da alfanun da ke cikin shi a halin yanzun ba shi da kwarjinin da da can ya ke da shi. A yanzun an fi karrama masu waƙa bisa ga marubuta, wannan kar ya karya masu qarfin gwiwa.

Mun gode.
Ni ma na gode.