Gwamnatin Neja ta sauya wa ‘yan gudun hijira 3500 sansani

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Jihar Neja ta sake wa wasu ‘yan gudun hijira a jihar su 3500 matsuguni zuwa Gwada Model Primary School a Juma’ar da ta gabata.

Waɗanda lamarin ya shafa ‘yan gudun hijira ne daga yankunan da ‘yan fashin daji da Boko Haram suka ɗaiɗaita a jihar kwanan nan.

A bayanin Gwamna Sani Bello ta bakin Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar (NSEMA), ya bada umarni a tabbatar ‘yan gudun hijirar na samun kulawar da ta dace na zaman da za su yi a sabon sansanin nasu har zuwa lokacin da komai zai daidaita kana a maida kowa asalin matsuguninsa.

Gwamnatin Neja ta sauya wa mutanen sansani ne tare da samar musu kayan masarufi na milyoyin naira da suka haɗa da kayayyakin abinci da makamantansu.

Gwamna Sani ya ce yana da yaƙinin nan ba da daɗewa ba ‘yan gudun hijirar za su koma matsugunansu saboda a cewarsa Gwamnatin Tarayya ta yunƙura tana aiki ba dare ba rana domin daƙile harkokin ‘yan ta’adda a faɗin jihar.

A Juma’ar da ta gabata, tsakanin ƙarfe 1 na rana zuwa 8 na dare, aka yi fama da jagilar ‘yan gudun hijirar daga IBB Primary School da ke Minna zuwa garin Gwada da wasu wurare.

Domin tabbatar da haɗin kai da kuma fahimtar juna, hukumar NSEMA ta haɗo kan shugabannin ƙabilar Gbagy da Fulani na yankin tare da sanya su cikin jami’an da aka ɗora wa alhakin kula da harkokin sansanin.