Kadafur ya zama muƙaddashin gwamnan Barno na kwana 21

Daga UMAR M. GOMBE

Majalisar Dokokin Jihar Barno ta amince da buƙatar Gwamna Babagana Umara Zulum inda ya nemi a naɗa mataimakinsa, Umar Usman Kadafur, a matsayin mauƙaddashinsa.

Zulum ya miƙa wannan buƙata ga majalisar ne domin ba shi zarafin tafiya hutu na kwana 21, kama daga ranar 29 ga Afrilu zuwa 19 ga Mayu, 2021.

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, Abdulkarim Lawan, ya ce tun a ranar 23 ga Afrilun da ya gabata gwamnan ya miƙa wa majalisar wasiƙar wannan buƙatar tasa, yana mai neman majalisar ta ba shi damar tafiya hutu na kwanaki 21.

Kazalika, Shugaban Majalisar ya ce gwamnan ya buƙaci majalisar ta amince ta naɗa Mataimakin Gwamnan jihar a matsayin Muƙaddashin Gwamna domin ba shi ƙarfin riƙon ragamar shugabancin jihar Barno, wanda hakan ya yi daidai da sashe na 190 (1) na Kundin Tsarin Mulki.

Gwamna Zulum, ya umarci mai magana da yawunsa, Malam Isa Gusau, ya sanar da ‘yan jihar wannan batu. Tare da kira ga ɗaukacin jami’ai da ma’aikatun gwamnatin jihar, da su bada cikakken haɗin kai ga wannan sauyi da aka samu.