Wata Guguwa

Daga AMINA HASSAN ABDULSALAM

Bayan fargaba da asarar rayuka da dunkiyoyi da annobar kwarona ta haddasa, rayuwa ta fara dawowa daidai a wasu wurare da dama, harkoki sun fara komawa kamar yadda aka san su. Farkon ɓullar wannan cuta mutane da dama ba su ɗau abin da muhimmanci ba, tunanin kowa shine cutar za ta tsaya ne a iyakar inda ta ɓulla kamar yadda aka saba, abu kamar wasa sai ga ta ta game duniya gabaɗaya ta buwayi duniya har ta illata tattalin arzuƙin mutane da ƙasashe da dama musamman ƙasashe masu tasowa da kuma talakawanta. Har yanzu ba wai cutar ta tafi ba ne ‘a’a tana nan sai dai an koyi yin rayuwa da ita, ta inda ake ɗaukar matakan kariya da kuma hanyoyin kauce mata.

Idan muka bar batun karyewar tattalin arziƙin ƙasashe musamman ma ƙasashe matalauta, za mu ga cewa ita wannan annoba da ta gauraye duniya gabaɗaya har ta sanya aka garƙame duniya, ta koyar da darussa da dama waɗan da za a daɗe ba a manta ba.

Kaɗan daga cikin darussan da ɓullowar annobar kwarona ta koyar sun haɗa, koya wa talakawa ko kuma masu ƙaramin ƙarfi tanadi. Ta koya wa jama’a da dama tsimi da tanadi: Da yawan mutanen a da ba su san tanadi don abinda ka iya je ya dawo ba, wasu sun rage almubazzaranci sun koyi tanadi sosai. Wasu mutanen kuma sun koyi tausayin na qasa da su ko kuma marasa ƙarfi ko marasa galihu, a cikin gararin annobar kwarona wani ya koyi yin kyauta domin an shiga halin da mutum yana gani ƙiri da muzu kuɗin sa ya gaza yi masa magani, yana gani ƙiri-ƙiri zai mutu ya bar dukiyarsa da kadarorinsa wasu su gaje.

Wasu ma’auratan a karo na farko sun fahimci irin alfanun da ke tattare da tattaunawa tsakanin mata da miji ko kuma iyali, wani bai taɓa zama da iyalinsa ba bare ya fahimci irin halin da suke ciki ko irin rayuwar da suke gudanarwa a bayan idonsa sai a karon dokar zaman gida. Zumunci ya inganta tsakankanin mutnane duk da dokar ba da tazara ko zaman gida da ake yi, tausayi da kyautayi sun sami ɗagawar darajojinsu. Yanayin ya bai wa yaran da ba su saba ganin ubansu ba damar saninsa a tsawon watanni da dama. Duk da cewa wasu na cewa zaman gidan ya sa an yi ta samun saɓani tsakanin ma’aurata masu ƙuntattaccen gida saboda yawan ganin juna da gwamutsuwar numfashin a halin babu, sai dai kuma kishiyar hakan ya fi yawa.

Garƙame ƙasa da aka yi ya tilasta wa mutane samin sababbin dabarun neman kuɗi walau ko ta hanyar amfani da yanar gizo ko kuma wasu hanyoyin, sababbin sana’oi na wucen gadi sun ɓulla sun kuma rufa wa mutane da dama asiri, duk da karyewar jari da ya sami wasu da dama.

Wasu gwamnatocin da suka gaza samarwa ƙasashensu ababen mora rayuwa sun rage dogaro da ƙasashen da suka ci gaba, sun fahimci gara su narka kuɗinsu a ƙasarsu musamman ma a ɓangaren lafiya da ilimi. Bugu da ƙari wasu kamfanoni sun fahimci cewa za su iya rage kashe kuɗi wajen gudanarwar harkokinsuna yau da kullum, ta yadda wasu daga cikin ma’aikatansu za su iya yin aiki daga gida na wasu ƙayyadaddun lokuta.

Tsafta ta inganta domin wasu rukunen mutane sun koyi wanke hannu sau ba adadi, sun koyi tsaftar jiki da ta muhalli da ta ‘ya’yansu, wasu iyaye musamman iyaye mata sun koya wa ‘ya’yansu wanke hannu a duk sanda suka dawo daga makaranta ko wani waje da ya danganci yin mu’amala da mutane ko abin hawa na jama’a. Wannan ya sa mutane sun daina sakaci da lafiyarsu. Hakan nan manyan wuraren taruwar jama’a don hada-hadar saye da sayarwa ko manyan kantuna ko guraren sufuri da zirga-zirga suna cikin tsaftace duk wani abu da za a tava kafin a shiga da bayan fitar mutane, kafin ma mutum ya shiga sai ya tsaftace hannayensa da sinadarin wanke hannu ko shafawa a ƙofar shiga wanda hakan wata tarbiya ce ta tsafta.

Hatta yaro ƙarami ya san ya nisanci duk wani mai tari ko atishawa saboda gudun kamuwa da cuta ko ba ta kwaronar ba ma, kusan sanya takunkumin hanci ya fara zama jiki domin duk wanda ya shiga cikin taro ba tare da ita ba, yana tare da barazana. Kasuwar takunkumin hanci da sinadarin wanke hannu ko shafawa sun samar da kuɗin shiga ga wasu jama’a ta inda suka haɗa jarin bunƙasa kasuwancinsu izuwa wani ɓangaren.

Talakawa sun gane cewa ashe gwamnati za ta iya magance matsalar rashin hasken lantarki, tsabagen handama da babakere ne ya sa ake hana talaka hasken wutar lantarki. An gane hakan a yayin da mahukunta suka ji tsoron bore a dalilin tsananta wa talaka da zaman babu cikin duhun duhunana.

Halin ha’ula’in da aka shiga ya sanya talakawan gari sun hankalta da sanya lura ga irin shuwagabannin da za su zaɓa nan gaba, domin halin zaman gida ya bankaɗa asirin wasu daga shuwagabannin da ba su da tausayin talakawansu ko kaɗan. Ɓoye tallafin abinci da wasu daga cikin shuwagabanni suka yi ya zubar da daraja da kimar wasunsu, adaidai lokacin da wasu ɗaiɗaikun hamshaƙai suka raba kayan tallafin rayuwa da hakan ya ɗaga darajarsu a idon mutane.

Da yawa daga cikin mutane sun koma ga Allah domin ganin yadda aka dinga zuba kamar ƙasa har ta kai kamar za a rasa wajen binne matattu. Sannan an rasa manya daga cikin al’umma waɗan da sune suka fi kasancewa cikin haɗarin kamuwa da cutar annobar kwarona bairos ɗin ko don wasu cututtuka da suke ta fama da su.

A ƙarshe kuma sai dai duk da waɗan nan darussan da aka samu har yanzu akwai ɓurɓishin illar da wannan yanayi ya samar, daga ciki akwai rasa madogarar cin abincin wasu, talauci ya ƙaru, rufe makarantu ya sanya karatun yara ya nakasa sosai, tattalin arzƙin ƙasa ta karye ko ta sami nakasa ko kuma ta ragu a wasu ƙasashe. Buƙatar abubuwan amfanin rayuwa sun ragu sannan kuma buƙatar abubuwan kula da lafiya sun ƙaru kuma babu su ko kuma ba su ishi kowa da kowa ya samu ba.

Babun da yunwar da aka yi fama da su sun ƙyanƙyashe sababbin ɓarayin unguwa da masu ƙwacen waya don su sayar su sami na saka wa a bakinsu, yau da gobe ta sanya waxan nan ɓarayi suka gawurta tun suna fakewa a duhun dare har ta kai yanzu da rana ƙiri-ƙiri suke ƙwacen.

Wagegen giɓin da ke tsakanin masu shi da mara sa shi ya sake ƙaruwa sabili da karyewar tattalin arziƙi, amma kam kowanne hali mutum ya sami kansa a wancan lokaci tabbas an koyi darussa da dama wanɗan da ba za a manta da su ba nan kusa.