Za mu tsige Buhari muddin magance matsalar tsaro ya faskara – Hon Bagos

Daga AISHA ASAS

Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar shiyyar Jos ta Kudu da Jos ta Gabas a Majisar Wakilai ta Ƙasa, Dachung Bagos, ya ce majalisa za ta ɗauki matakin tsige Shugaba Muhammadu Buhari muddin Majalisar Zartarwa ta Kasa ta kasa kawo ƙarshen matsalolin tsaron da suka addabi ƙasa.

Ɗan majalisar ya yi wannan furuci ne yayin wani shiri da aka yi da shi a wannan Alhamis ɗin a tashar talabijin ta Channels.

Idan dai za a iya tunawa, ko Larabar da ta gabata sai da majalisar ta kafa wani kwamiti na mutum 40 tare da ɗora masa aikin binciko hanyoyin da za a bi don magance ƙalubalan tsaron da suka yi wa ƙasa tarnaƙi.

Tuni dai kwamitin ya shirya gudanar da babban taro na yini huɗu ya zuwa watan Mayu mai zuwa, a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin sauke nauyin da aka ɗora masa.

Yayin tattaunawar tasu, Bagos ya ce za a soma shirin tsige Shugaba Buhari ne idan Majalisar Zartarwa ta ƙi yin aiki da shawarwarin da za su cim ma bayan kammala babban taronsu da wasu watanni.

A cewarsa, “Muna da ikon da za mu iya tsige shugaban ƙasa idan ya zamana cewa ba zai iya ci gaba da tsare rayuka da dukiyoyin ‘yan Nijeriya ba.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *