Jami’ar Edusoko mafita ce ga ɗaliban Neja masu neman gurbin karatu – Gwamna Bello

Daga BASHIR ISAH

Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja, ya ce kafa Jami’ar Edusoko zai taimaka wajen magance ƙalubalen samun gurbin karatu da ake fama da shi a jihar Neja.

Gwaman ya bayyana haka ne sa’ilin da ya karɓi baƙuncin Kwamitin Amintattu na Jami’ar Edusoko ƙarkashin jagorancin Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar, a fadar gwamnatin jihar da ke Minna.

Ya ce akwai ɗimbin ɗalibai a jihar Neja da ke neman gurbin karatu a jami’a, yana mai cewa zuwan Jami’ar Edusoko zai zama mafita ga ɗaliban.

Baya ga yaba wa Etsu Nupe bisa ƙoƙarin samar da wannan jami’a, Gwamna Bello ya ce yana da tabbacin jami’ar za ta yaye ɗalibai waɗanda al’umma za ta amfana da su.

A nasa ɓangaren, shugaban kwamitin Mai Martaba Sarkin Bida, Alhaji Yahaya Abubakar, ya ce sun ziyarci Gwamna Bello ne domin gabatar masa da lasisin kafa Jami’ar Edusoko da suka samu daga Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) domin karantarwa a matakin digiri a matsayin jami’a mai zaman kanta a jihar.

Basaraken ya shaida wa Gwamnan cewa tuni jami’ar ta soma shirye-shiryen ɗaukar ɗalibai ‘yan aji ɗaya ta hannu hukumar JAMB, inda nan ba da daɗewa ba za a fitar da jerin sunayen ɗaliban da suka yi nasarar samun gurbin karatu a jami’ar a shafin intanet na jami’ar.

Haka nan, Sarkin ya yi yabo da jinjina ga gwamnan jihar bisa irin rawar da ya taka wajen neman kafa jami’ar. Kana ya yi kira a gare shi da ya ci gaba da mara wa jami’ar baya yadda ya kamata.

Tawagar kwamitin ta ƙunshi mambobi irin su Alhaji Dalhatu Aliyu Makama, Makaman Nupe, Farfesa Muhammad Alkali, Mataimakin Shugaban Jami’ar, Alhaji Aliyu Ndagi da sauransu.