Gwamnatin Tarayya ta bayyana 3 ga Mayu, ranar hutun ma’aikata

Daga WAKILINMU

Gwamnatin Tarayya ta ayyana Litinin mai zuwa, 3 ga Mayu, 2021, a matsayin ranar hutun ma’aikata albarkacin bikin Ranar Ma’aikata ta Duniya na bana.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Ogbeni Rauf Adesoji Aregbesola, shi ne wanda ya sanar da hakan a madadin Gwamnantin Tarayya, inda ya yi amfani da wannan dama wajen taya ma’aikata a Nijeriya murnar zagayowar wannan rana.

Ministan ya jinjina wa ɗaukacin ma’aikata bisa irin haƙuri da juriya da fahimtar da suke nunawa haɗa da goyon bayan da suke bai wa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari a ƙoƙarinta da take yi na ciyar da ƙasa gaba da bunƙasa ta.

Aregbesola ya yi kira ga kafatanin ma’aikata na Nijeriya gami da ƙungiyoyin ƙwadago da su ci gaba da gudanar da ayyukansu yadda ya kamata. Yana mai cewa duka matsalolin da ake fuskanta a yau za su zama labari nan gaba.

Ya ce gwamnati ba ta ɗauki lamarin tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa da wasa ba.

Ta bakinsa, “Gwamnanti na ci gaba da ɗaukar ingantattun matakai da dabarun da suka dace wajen ganin ta daƙile duka ƙalubalen tsaron da suka dabaibaye ƙasa. Don haka ina kira ga Ƙungiyar Kwadago da ma’aikata da kowa ya bada gudunmawarsa wajen yaƙi da matsalolin tsaron ƙasa.”