An cafke ‘yan fashi 6 ɗauke da shanu 183 da kuɗi dubu N268 a Oyo

Daga AISHA ASAS

Rundunar tsaro ta musamman a jihar Oyo mai ƙunshe da ‘yan bangan OPC da Amotekun da VGN, ta cafke wasu mutun shida da ake zargin ‘yan fashin daji ne a safiyar Alhamis da ta gabata ɗauke da shanu 183 a yankin ƙaramar hukumar Kajola ta jihar.

A cewar Kwamandan Amotekun na jihar Oyo, Col Olayinka Olayanju (mai murabus), ya ce an kama waɗanda ake zargin ne a hanyar Okeho zuwa Ilua da kuma hanyar Okeho zuwa Iseyin da misalin ƙarfe 4 na asuba na wannan rana.

Kwamandan ya ce sun kama ɓarayin ne bayan ɗauki ba daɗin da aka yi da su a wuraren da suka kafa haramtattun shingayen bincike a kan hanya suna cutar da jama’a.

Ya ci gaba da cewa sun yi amfani da shanun da suke korawa ne suka fake a matsayin su makiyaya ne, tare da yin amfani da wannan dama wajen cutar da jama’a a kan hanya.

A cewar kwamandan baya ga shanun da aka kama su da su, an kuma gano wasu makamai da suke ɗauke da su da kuɗi N268, 470.00.

Col Olayanju ya ce waɗanda kamen ya shafa su ne, Awali Atine, Ibrahim Abu, Shuaib Balau, Ibrahim Musa, Abdullah Masika da kuma Umar Aliu Masika.

Haka nan, ya ce jami’ansu na ci gaba da bin sawun waɗanda suka tsere a lokacin kamen. Tare da cewa an miƙa waɗanda suka shiga hannu da abubuwan da aka gano a wajensu ga hukumar ‘yan sanda na yankin Okeho don ci gaba da bincike.