Sanata Ordia ya tsallake rijiya da baya sau biyu a yini guda

Daga FATUHU MUSTAPHA

Har sau biyu ‘yan bindiga na kai wa Sanata Clifford Ordia (PDP Edo ta Tsakiya) hari a Litinin da ta gabata a hanyar Okenne zuwa Lokoja da kuma hanyar Lokoja zuwa Abaji.

Sanata Ordia wanda shi ne shugaban kwamitin Majalisar Dattawa kan Basussukan Cikin Gida da Waje, ya yi wa manema labarai bayanin yadda ya kuɓuta daga harin ‘yan bindigar da suka buɗe wa tawagar motocinsa wuta a kan hanyarsa ta komawa Abuja daga jihar Edo.

Ya ce sakamakon musayar wuta da aka yi tsakanin jami’an tsaron da ke ba shi kariya da ɓarayin, wasu ‘yan sanda su uku sun ji rauni.

Yana mai cewa ɗaya daga cikin jami’an wanda ya samu mummunan rauni na ci gaba da samu kulawa a wata asibitin Abuja.

Ya ci gaba da cewa ‘yan fashin sun yi wa motarsa ruwan alburusai, amma ya samu ya tsira ba tare da ko ƙwarzane ba.

Da yake zurfafa bayani kan abin da ya faru, Sanatan ya ce, “Na yi matuƙar kaɗuwa da abin da na gani.

“Da muke dawowa daga Edo a wani wuri tsakanin Okenne da Lokoja inda a nan muka yi arba da ‘yan fashi. Nan take suka buɗe wa tawagata wuta inda su kuma ‘yan sandan da ke tare da mu suka maida martani.

“Yayin musayar wutar ‘yan sanda uku sun ji rauni inda muka hanzarta kwashe su zuwa Babbar Asibitin Tarayya (FMC) da ke Lokoja, jihar Kogi.

“Jami’an sun yi ƙoƙarinsu wajen tarwatsa ɓarayin. Ba tare da ɓata lokaci ba na kira Babbar Asibitin Tarayya da ke Abuja a kan su kasance cikin shiri. Guda daga cikin jami’an ya samu mummunan rauni.

“Mun sake yin arba da ɓarayin (karo na biyu) ne a wajajen Abaji. An samu tsaikon zirga-zirgar ababen hawa sakamakon abin da ya faru ga shi kuma muna sauri mu kai jami’in da ya ji rauni asibiti, ganin haka sai muka yanke shawarar mu canza hanya. A nan ma suka sake buɗe mana wuta. Sai da wasu ‘yan bijilanti suka kawo ɗauki kafin daga bisani aka kora su daji.

“Yadda aka yi na tsira kenan daga harin. Idan ka ga motocina za a ga yadda aka yi musu fata-fata da alburusai. Amma na ji daɗi kasancewar baki ɗayanmu mun tsira. Ya zama tilas in yaba da bajinta ‘yan sandan da ke tare da mu. Za su iya fiye da haka wajen bai wa ‘yan Nijeriya kariya.”

Daga nan, Sanatan ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta ɗaukar matakin sake fasalin tsaron ƙasa, tare da gargaɗin cewa yanzu fai babu wanda ya tsira a ƙasa.