Majalisa ta yi kumfar baki kan yadda tsaron Nijeriya ya dagule

Daga UMAR M. GOMBE

Majalisar Dattawan Nijeriya ta bayyana cewa taɓarɓarewar tsaron ƙasa abin kunya ne ga Nijeriya. Majalisar ta bayyana haka ne a zamanta na Talatar da ta gabata, inda sanatoci da dama suka nuna takaicinsu kan mummunan halin da tsaron ƙasa ya faɗa.

Sa’ilin da yake tofa albarkacin bakinsa a muhawarar da aka tafka a zauren Majalisar, Sanata Birma Enagi (APC Neja ta Kudu) ya ce, “Tabbas lamari ya lalace kuma abin kunya ne. Gwamnatin Tarayya ta yi sakwa-sakwa wajen yaƙi da ɓarayin daji da ‘yan Boko Haram.”

Ya ce, “Mafi takaicin abin da ke faruwa shi ne babu wani ƙwaƙƙwaran mataki da gwamnatin tarayya ta ɗauka wajen daƙile wannan matsala. Ya zama wajibi Majalisar Dattawa ta duba sannan ta samar da ingantaccen matakin da ya kamata a ɗauka.”

Shi ma Sanata Smart Adeyemi (APC Kogi ta Yamma) bai rasa ta cewa ba kan matsalar, yana mai cewa, “Ya zama dole Shugaban Ƙasa Muhamnadu Buhari ya yi tsayin daka. Ƙasa ta dagule. Ba zai yiwu mu ci gaba da yin shiru ba sabida fannin tsaron ƙasa ya taɓarɓare. Muna buƙatar taimako daga waje don magance wannan matsala da ta zama abin kunya ga ƙasa.”

Haka dai Majalisar ta ɗauki zafi inda sanatoci da dama suka nuna damuwarsu da kuma buƙatar gwamnati ta miƙe ta yi wani abu a kan matsalar tsaron da ta ƙi ci, ta ƙi cinyewa.

Da yake bayani, Shugaban Majalisar, Ahmad Lawan, ya ce babu shakka Nijeriya na fama da matsananciyar matsalar tsaro wadda ke buƙatar haɗin kan kafatanin ‘yan Nijeriya domin daƙile ta.

“Wannan abu ne da ya shafi kowa a ƙasa. A namu ɓangaren mu da muke a Majalisar Ƙasa, dole mu ware kason kuɗi domin shirin samar da ƙarin dakarun sojoji da ‘yan sanda”, in ji Lawan.

Shugaban Majlisar ya bada tabbacin cewa za a tabbatar da aiwatar da abubuwan da aka cim ma a zauren majalisar ba tare da ɓata lokaci ba.

‘Yan majalisar sun cim ma matsaya a kan za su buƙaci dukkan shugabannin fannin tsaro da su gaggauta tura jami’an tsaro zuwa yankunan da lamarin ya shafa domin dawo da lumana da kuma saka ƙwarin gwiwa a zukatan al’ummomin yankunan.

Majalisar ta ɗauki zafi ne biyo bayan ƙorafin da Sanata Sani Musa (APC Neja ta Gabas) ya gabatar wa majalisar kan yadda harkokin ‘yan fashin daji da Boko Haram suka mamaye wasu sassan Jihar Neja, musamman ma a yankunan ƙananan hukumomin Shiroro da Munya da kuma Rafi. Lamarin da a cewar sanatan ya yi dalilin raba dubban jama’a da gidajensu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *