Tallafin Sadiya Farouq a kan Korona

Sadiya

Daga IBRAHIM SHEME

A bara ne aka samu ɓullar cutar nan mai suna ‘Coronavirus’ (COVID-19 a taƙaice), wadda da Hausa ake kira Korona. Cuta ce wadda ta mamaye duniya, ta zama annobar da mu dai a zamanin mu ba mu taɓa ganin irin ta ba. Ta tsiro ne daga birnin Wuhan da ke yankin Hubei na ƙasar Chaina inda daga can ta yaɗu a faɗin duniya. Ta tilasta rurrufe wurare tare da jawo bala’o’i da su ka haɗa da yawan mace-mace, rashin samun kuɗin shiga, hana tafiye-tafiye, rufe masana’antu da wuraren kasuwanci, rasa aikin yi, da kuma tsananin fargaba.

Bala’in Korona ya fi shafar ƙasashe masu raunin tsarin tattalin arziki irin Nijeriya. A cewar Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), kashi 40 cikin ɗari na ‘yan ƙasar nan su na rayuwa cikin fatara ne, domin kuwa a cikin wannan ƙididdigar babu mai iya samun N137,430 a shekara, wanda hakan na nuna cewa a cikin kimanin mutum miliyan 82.9 babu mai iya samun abin da ya kai dalar Amurka ɗaya a rana.

An fara samun wanda ya kamu da korona a Nijeriya a ƙarshen Fabrairu, 2020. Don haka sai Gwamnatin Tarayya ta yi sauri ta fito da wasu tsare-tsare da su ka haɗa da wayar da kan al’umma, da hana zirga-zirga da kuma wasu shirye-shiryen harkar kuɗi don magance matsalar abinci. Duk da yake an kafa kwamitin shugaban ƙasa da zai gudanar da aikin aiwatar da tsare-tsare kan matsalolin da cutar ta haifar, to amma sai aka ga cewa Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa ta Tarayya ta na da muhimmiyar rawar da za ta taka a kan matsalar. Hasali ma dai annobar ta kawo wa ma’aikatar babban aikin ta na farko, domin kuwa ba a fi watanni da gwamnatin Buhari ta ƙirƙiro ta ba. Hakan ya ɗora babban nauyi a kan Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq. 

A daidai lokacin da Korona ta ɓarke, tattalin arzikin Nijeriya na cikin murmurewa daga masassarar da ta same shi a 2016 sakamakon faɗuwar farashin man fetur a tsakanin 2014–2015. A wani rahoto da Bankin Duniya ya buga a cikin 2019, an ce wannan karayar tattalin arziki, wadda ita ce ta farko a cikin shekaru 25, ta haifar da tsukewar tsarin tattalin arziki. To, ana kukan targaɗe sai karaya ta zo; annobar Korona ta maida hannun agogo baya, ta maida ƙarin mutum miliyan 17 faƙirai, musamman mazauna birane. Masana sun lura da ƙaruwar fatara da ta faru a kashi na biyu na shekarar 2020 a lokacin da ake aiwatar da dokokin magance Korona. Saboda haka ‘yan Nijeriya, musamman waɗanda annobar ta fi shafa kai-tsaye, sun sa ido su ga irin tallafin da ma’aikatar Sadiya za ta kawo masu.

Gwamnati ta kawo tallafin ta hanyoyi daban-daban. Ma’aikatar ta fara da fito da dabarun rage tsananin da yanayin ya haifar musamman ga mutanen da su ka fi fatara a cikin al’umma. Sun haɗa da ‘yan gudun hijira da waɗanda rikice-rikice su ka kora daga ƙauyukan su, naƙasassu, dattawa, mutanen da aka sace, marayu, faƙirai a cikin al’umma, masu ƙananan sana’o’i da sauran su.

Don cimma wannan buri, ma’aikatar ta raba kayan abinci irin su shinkafa, masara, gero, dawa, man girki, tumatirin gwangwani, madara, suga da taliya ga mabuƙata a jihohi da Yankin Birnin Tarayya (FCT).

Ta fito da shirin bada kyautar kuɗi inda ake ba mutane kuɗin wata huɗu a lokaci guda. Haka kuma ta bada rance maras ruwa na wata uku ga waɗanda ke cikin shirye-shiryen bada lamuni na ‘TraderMoni’ da ‘MarketMoni’.

Ta raba abinci ga da ya haɗa da shinkafa, wake, man girki, man ja, ƙwai da gishiri a gidajen ‘yan makaranta da aka rubuta sunayen su a shirin ciyar da ɗalibai na ƙasa.

Haka kuma Gwamnatin Tarayya tare da haɗin gwiwar Shirin Bada Abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya (WFP) sun bada tallafin tsabar kuɗi da abinci a biranen da korona ta fi shafa. Wani haɗin gwiwar da ma’aikatar da WFP su ka yi shi ne na samar da abinci da kuɗi a jihohi uku da Korona ta fi shafa, wato Kano, Abuja da Legas, inda aka kashe dalar Amurka miliyan 4; yayin da gwamnati ta samar da hatsi, ita kuma WFP ta samar da kuɗi. An ce wannan tsari ya isa ga miliyoyin mutane a biranen da matsalar hana zirga-zirga ta fi ta’azzara.

Bayan wannan akwai shirin Lamuni ga Matan Karkara wanda ma’aikatar ta ƙirƙiro a bana a matsayin wani sashe na shirin Shugaba Muhammadu Buhari na rage fatara da yunwa. An yi shirin domin matan karkara 120,000 a dukkan ƙananan hukumomi 774 na jihohi 36 da Abuja. Shiri ne inda ake so mata ‘yan tsakanin shekara 18-50 su riƙa karɓar N20,000 kowaccen su. Manufar shirin ita ce a inganta hanyar samun kuɗin shiga, a samar da abinci, kuma a ba mutane abin yi.

Sadiya Umar Farouq ta riƙa gudanar da waɗannan shirye-shirye bilhaƙƙi da gaskiya. Ana ganin ta a jihohi daban-daban inda ta ke ƙaddamar da su da kan ta. Bayanai daga waɗanda su ka amfana sun nuna cewar abin da gwamnati ke yi kan Korona ya dace sosai.

Masana harkokin tattalin arziki sun yi amanna da cewa in da ba a shigo da waɗannan tsare-tsaren ba, to da talakawan Nijeriya sun fi gasuwa, musamnan tunda wannan annoba ta ƙara jefa su cikin matsi. Tallafin da aka kawo ya taimaka wajen rage raɗaɗin rayuwa da ake ciki.

To amma fa har yanzu ‘yan Nijeriya su na cikin halin ƙunci na fatara da yunwa. Masana sun ce Nijeriya ta fi kowace ƙasa yawan faƙirai a dukkan yankin yammacin Sahara tun ma kafin zuwan Korona. Haka kuma har yau annobar Korona ba ta kau ba duk da yake ana ta allurar rigakafi. Saboda haka har yau akwai buƙatar ci gaba da aiwatar da waɗannan shirye-shirye na tallafa wa jama’a.

A ƙarshe, ya kamata gwamnati ta sa ido tare da buɗe kunne kan sukar da wasu ke yi na cewar an siyasantar da bada tallafin, kuma ana satar kuɗin tallafin. Ya kamata gwamnati ta binciki wannan zargin, kuma ta magance duk wata matsala. Tabbatar wa da jama’a cewa babu wata ƙumbiya-ƙumbiya a waɗannan shirye-shiryen zai ƙara wa Minista Sadiya Farouq da ma’aikatan ta martaba a idon jama’a a ƙoƙarin su na isar da tallafin gwamnatin Buhari ga mabuƙata.